Bin Muhammad
2022-11-20 KD
Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Paul Merson, ya shawarci kocin Ingila, Gareth Southgate, da kada ya yi amfani da Mason Mount na Chelsea, da Kieran Trippier na Newcastle United, a wasan farko na gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2022, da Iran a ranar Litinin.
A cewar Merson, ba a bukatar Mount da Trippier a lokacin da Ingila za ta kara da Iran, ya kara da cewa zai kasance wasa mai tsauri ga tawagar Ingila saboda Iran tana da babban koci Carlos Queiroz. Merson ya shaidawa 'Daily Mail'.
Ingila tana rukuni na biyu a gasar cin kofin duniya kuma za ta kara da Iran, Wales da Amurka.
Tags:
Labarin wasanni
Kaji kasan muminai kenan tako,ina tayiwa kasa yahudawa nisa
ReplyDelete