WANI HALI NA MATAR ƘWARAI...

 



Mijin ya kalle ta ya ce: "Wallahi yau ban samo komai ba Gimbiyata. Na bubbuga ko'ina babu. Buhariyya ta sa kowa a gaba."


Matar ta ce: "Maigida ai kowa ya san babu. 'Dazun nan wata qawata ta zo take roqona don Allah in taimake ta ko da da rabin mudun shinkafa ne, kwanansu biyu ke nan ba su d'ora girki a gidansu ba. Jikina na rawa na raba ragowar dankalin Hausar nan na ba ta. Sauran ne na dafa mana. Na kar'bo quliquli a maqwabta na daka don mu ji dad'in ci. Ashe ke nan ka ga gara ma mu muna da abin ci. Don haka kada ka damu wallahi."


Mijin ya yi shiru yana mamakin hikimar tattali irin na matar nan tasa.


Ita kuma ganin ya yi shiru sai take ce masa: "Tunanin me kake Maigida? Ba dai na abincin gobe da safe ba? Kada ka ji komai Allah yana nan. Zai zo mana da d'auki ta inda ba ma zato."


Mijin ya yi murmushi. Bakinsa ya furta godiyarsa ga Allah a bayyane. Ya kuma qara da cewa: "Allah ya yi miki albarka Gimbiyata."


"Allah ya yi mana albarka baki d'ayanmu Maigida." Ta fad'i haka a lokacin da take miqewa daga inda take zaune. 


Ta kawo masa abin da ta ce ta dafa cikin tsabtataccen kwanukan ci da na sha. Ta zauna a gefensa a lokacin da yake ci, ita kuma tana shaida masa godiyarta ga Allah da ya ba ta shi a matsayin miji kuma mai damuwa da matarsa. Ta ce da yawa daga cikin qawayenta har yanzu sam ko mijin ba su da shi bare har su yi haqurin rayuwa. Ashe ke nan ita sai dai ta yi godiya ga Allah da ya ba ta.


Mijin yana ci kunnuwansa na sauraronta, zuciyarsa kuma na tuno masa irin rigimar da Abokinsa Haruna ya fad'a masa cewa sun yi da matarsa a kan wai ita ta gaji da cin abinci babu nama. Wai ta qirga mako guda ke nan suna cin abinci a gidan nan babu nama. Don haka ita ba za ta iya ba. Abokin ya ce a ranar matar tasa kwana ta yi a gidansu. Ta yi yaji. 


Ya je biko amma sai ya samu iyayen suna mara wa 'yarsu baya. Yanzu haka dai auren yana shirin rushewa. Domin matar ta ce ita dai ba za ta iya ba.


Yayin da mijin ke wannan tunani, ita kuwa matarsa a bayan ta d'an yi shiru don kada ta dame shi saboda ganin kamar zuciyarsa na tunanin wani abin, sai ta fara lissafin yadda za ta tashi tun da asuba don dakan geron da za ta yi mu su kunu da safe da shi. Su sha ko ba sukari. Tunaninta ya ba ta cewa hakan ne kad'ai mafita tunda dai babu ko da sisi a gidan.


Tsakure daga taskar MBI

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post