©Shahid Mahmud Library.
+2348068811025
*Yaushe ne ya wajaba akan yarinya ta tsayu da wajiban shari'a?*
Wajibi ne ga yarinya bayan ta riski Taklifi ta tsayu da wajibanta na sharia, Wanda takalifin ke aukuwa da tabbatar ababe uku kaman haka;
~Cika shekaru 9 bisa lissafin Hjijiryya.
~Hankali, don haka sharia bata sanya aiki akan maras hankali ba, Ma'anar hankali anan shine Ikon banbance abubuwa.
~Kudra (Iko) don haka be wajaba ga Yarinya (wacce ta riski Taklifi) tazo da wajiban da Bazata Iya zuwa dasu ba, saboda raunin jikin ta ko lalura.
*Shin ɗaura waɗannan wajiban a kan yarinya bazai zama ɗaura mata abinda Ya zarce ikonta ba?*
~Shari'ar musulunci shari'ace me sassauci, taklifin be zarce qudrar ta ba matukar dai ta riski shekarun taklifi (balaga).
Na'am akan samu wasu lokuta ta gaza tsayuwa d wajibanta kaman azumi, to anan wajabcin azumin kan sauka akanta a wannna watan sai ta ramashi a watanni da zasu Biyo shi kafin zagayowar sa.
In kuma ta gaza ramawa har zagayowar wani ramadan ɗin, wajabcin sa duka Ya sauka akanta, sai ta lizamci ciyarwa, Ta hanyar ciyar da Mabukaci 1 kowani yini mikdarin 3/4 na Kilogram, ba kuma wajibi ne a gareta ta rama ba koda kuwa ta samu Ikon hakan daga baya.
Yake yar uwata kisan Allah be ɗoramiki wani abu ba face saida ya tabbatar da zaki Iya, don haka sallah d azumi da kumusi da hajji da sadaka d amana, da barin gulma da annamimanci da sata da sauran su duka abubuwa ne da kowa zai Iya, amma d zaran wani lalura ya Bijro to an sauke Miki wnnnan wajibin, kaman Yanda Allah ke fadi (Allah baya ɗorawa wata rai wani abu aiki Face sai abinda zata Iya).
Zamuci Gaba.........