Inji Shaikh Ibraheem Zakzaky a yayin ziyarar Dandalin Matasa
“(Dole) Ya zama hadafinmu shine tabbatan addini. Wasu sun yi kokari iyakar iyawarsu su canza hadafin Harka, ya zama kamar hadafin Harkar shine ana cema mutane ne su zama Shi’a, shikenan illa-iyaka, kai Shi’i ne an gama. To ba shine hadafin Harka ba. Hadafin Harka shine tabbatan addini.
In kai Shi’I ne shikenan kai Shi’i ne, sai a yi abubuwan da suka shafi Shi’a da kai. In ma ba Shi’i bane za a tafi da kai, ko kai Sunni ne. Ko kai Salafi ne ma, in dai ka yarda addini ya tabbata, kuma ka yarda addini ya tabbata (shikenan).
Na ji ana hira da wani Basalafe a gidan Talabijin Al’arabiyya, ya zo da littafai a gabansa ya aje, ya tsaya tsayin daka cewa lallai Salafiyya ba sa kafirta Musulmi. Yace sam! (Basu yi). Sai mutumin (da ke jan shirin) yace masa to Shi’a Musulmi ne? Yace eh, musulmi ne. Sufaye ma Musulmi ne? Yace Musulmi ne.
Nace to kai wannan Salaf din naka lallai ya yi daidai. Mu nan namu Salaf-Salaf ne. (Kamar) wani ya yi wake yake cewa wai, shi yana son miyarsa da magi, baya sonta salaf-salaf. Wato kenan in kai Salaf din naka yana nufin kai ka soke komai mai kyau ne, kace in ba kai ba babu Musulmi, (kamar yadda wasu suke cewa in ba su ba kowa ba Musulmi bane). To, in dai ba irin wannan I’itiqadin kake da shi ba, in dai kana ganin sauran musulmi ma su Musulmi ne amma kuna da bambancin fahimta, to falillahil Hamd, za a tabbatar da addini.
Addini zai zama na kowa da kowa ne, ba addinin Shi’a daban, addinin Sunnah daban ba, addini daya ne. Ba Alkur’anin Shi’a daban, Alkur’anin Sunnah daban bane, in dai ba wawan gari ne ba ba mai fadin wannan. To kuma in an zo fassarar Alkur’ani ko tsakankanin Sunni da Sunni ana samun sabani, ko ba haka bane? Haka kuma tsakanin Shi’a da Shi’a ana samun sabani, saboda haka a hadu ace ga mafita, wannan ya fadi ra’ayinsa, wancan ya fadi ra’ayinsa a yi ittifaki a kan abu, wani abu ne da aka san shi. Saboda haka hadafi shine tabbatan addini, kuma addinin nan da kowa za a yi shi, kowa da kowa.
To, tana iya yiwuwa mutum yace, to shi tabbatan addinin nan ai ba zai yiwu ba. Na sha yin wannan maganar a ‘public’ ma. Wasu suna cewa ba zai yiwu bane. To, tambaya, in abu ba zai yiwu ba ana barinsa ne? Ina tambaya ne, ana fasawa ne? Akwai wata maganar Hikima da ake cewa: “Abin da ba za a riske shi gaba daya ba, ba a barinsa gaba daya.” Idan ba zai yiwu addini ya tabbata ba, ko mun jajirce mun ce sai addini ya tabbata, sam ba zai yiwu ba. To duk da haka za mu bida, don abin da aka kallafa mana kenan.
Ina tambaya; Da Allah Ta’ala ya turo Annabawa, ya turo su don su yi mene ne? Don su shiryar da mutane su zo a tafarkin addini. To, Allah Ta’ala ya turo Annabi Musa zuwa ga Fir’auna, tana iya yiwuwa Fir’auna ya musulunta, jama’arsa ma su musulunta duk su zama daidai? Tana iya yiwuwa, amma kuma tana iya yiwuwa kuma ba zai yiwu ba.
A sanin Allah Ta’ala (tunda shi ya san abin da zai faru) Fir’auna ba zai Musulunta ba, amma yana da hakkin a kira shi. Sai Allah Ta’ala yace da Annabawansa (Musa da Haruna (AS): “Waqula lahu qaulan layyinan la’allahu yatazakkaru au yakhsha.” Aka je kuma aka masa ‘Qaulan layyin’ (magana tattausa), aka tausasa masa murya, amma duk da haka dai ya butulce, aka kawo duk ayoyi amma ya butulce. Yace Musa, ina ganin an maka sihiri ne.
Annabi Musa yace, kai Fir’auna ka san duk wadannan ayoyin ba wanda ya saukar da su sai Ubangijin sama da kasa, kai dai ina ganin kai Fir’auna kai dai tababbbe ne kawai. Fir’auna ya sani sarai, amma sai “suka musanta duk ayoyin da suka gani, amma a zuciyarsu sun san da gaske ne.” Haka Allah ya fada. Wato a ransu sun san Musa din nan gaskiya ne Allah ne ya aiko shi, amma basu bi ba, saboda taurin kai da dagawa.
To amma ka ga sai da aka kira su, ba a ce Musa yaje kawai ya halaka su ba, su suka halaka kansu da kansu. Da aka ce Annabi Musa ya fita, sai suka bi shi, su suka halaka kansu da kansu. Amma ka ga an yi musu duk abin da za a iya yi (na kira, amma ba su bi ba), har izuwa karshe (sannan aka halaka su).Ka ga kenan, ashe idan ba za a cimma buri ba, ba ana fasawa bane. Da tun farko da zuwan Musa ba bukatar ya yi wa’azi, tunda ya san Fir’auna ba zai Musulunta ba, sai yace kawai Banu Isra’ila ku zo mu yi ta Musuluncinmu, mu kyale Fir’auna tunda shi ba zai taba Musulunta ba. Su ce to me za mu yi ma Fir’auna? Yace mu je mu gaishe shi mu ce Ranka ya dade, Allah kara yawan rai, muma a dan sammana abin da ake samma mutane.
Abin da wasu suke cewa kenan, abin da kuma suka yi kenan, su dai su zauna akawai ace musu suna addininsu, a karbe su kuma a dan yanko musu nasu, da burodinsu da dan man-shanunsu su shasshafa, su ci abinsu.
Ta almaran mutanenmu suna cewa, wai in Dujjal ya bayyana, wai idan mutum bai bi shi ba zai tursasa shi, amma in ya bi shi, wai shi dokin Dujjal yana kashin masa ne, yana fitsarin zuma, to sai ya bashi wannan masa da zuman ya rika ci. Nace Tir! Ba fa Hadisi ne ya zo da shi ba, amma kinayar wannan in ka bi Dujjal karshe me za ka ci? Kazanta. To haka nan ne.
Fi’ilan ba kashin doki ne da fitsarin doki kake ci ba, amma dai kazantan da kake ci ya wuce wannan ma, saboda haramun ne da aka tattaro aka mika maka. A kwaso harajin da aka saka ma Kidnappers kaima a baka. Don an fahimci Kidnapping din nan da yaran suke yi, manyan ke karbar miliyoyin. To kai kuma in kai Malam ne, kana cewa a zauna lafiya lau ba wata matsala. Sai a ce Malam ga dan abin da aka samu na Kidnapping, kai ma sai a sammaka. Ka ga wannan ba kashin doki bane da fitsarinsa? Ma’ana kazanta ne. Sai a tattaro kazanta a mika maka kai ma, ka zauna lafiya tare da su. To abin da ake so kenan, ka zauna lafiya.
To da haka nan ne, sai Annabi Musa ya zo kawai ya kira jama’arsa kawai su yi addininsu su yi shiru, ba za su ce Fir’auna ya zo ya bi ba, saboda ba zai bi ba. Ba za su ce jama’ar Fir’auna ku zo ku bi ba, saboda ba za su bi ba.
To haka nan kuma, shi Manzon Rahma (S) da ya zo Makkah, ya kira mutanen Makkah shekara 13 suna ta bashi wahala, duk wanda ya yi imani sai a tursasa shi. To tunda wasu sam basu yi imanin ba ma sam har suka mutu, to sai a fasa? Sai ya fasa da’awa? Sai aka ce ai wannan ba za su yi imani ba, fita kawai ka bar garin ko kuma ka zauna tare da su, kai kai addininka su su yi nasu ku yi zamanku lafiya kasa daya? Ka yi musu biyayya don ku zauna lafiya? Abin da wasu ke kokarin su ce kenan.
In wannan ne, ba bukatar ma tun farko a yi Harka din. Tun farko babu bukatar kai Harka din. Duk wanda yace, manufarmu ba shine addini ya yi iko ya kafu daram a kasar nan ba, to ya fa yi ritaya ne daga gwagwarmaya. Shi ba dan Harka bane, ya yi ritaya, ya yi ‘resignation’ tuntuni.
Kana cewa ai yanzu abin da ke gabanmu ba shine a tabbatar da Hukuma Islamiyya ba, ba ma dole bane, to kawai ka riga ka yi ‘resigning’, sunanka tsohon buraza. Ka zama tsohon Buraza. Ko ba haka ba? Burazan da kenan. Da can dan gwagwarmaya, yanzu-yanzu ya yi ritaya.
Kun san duk wadanda suka yi ritaya haka suka rika cewa? Ko baku san wadanda suka yi ritaya ba? akwai wadanda suka yi ritaya basu ce su Shi’a bane, suka ce Shi’a ake yi, kuma ba za su yi Shi’a ba, sai suka yi ritaya, suka ce za su yi gwagwarmaya ne amma a tafarkin Sunnah ba Shi’a ba, sai muka karata muka ga inda suka kare, kun ga inda suka kare ko? Sun zo sun zama yaran mahukunta din, suna samun nasu, suna cin masansu da zuma (kun san inda masan da zuman ya fito ko?), lafiya lau suka yi zamansu.
Sai kuma wasu suka ce su Shi’a ne, amma ba gwagwarmaya, suma suka koma waje daya suka yi zamansu suna cin masansu da zuma lafiya lau. To kai ma in kace kana cikin gwagwarmayar baka fita ba, amma kace ba tabbatar da addini za a yi ba, to je ka karbi masarka da zumanka kawai, don ka riga ka yi ritaya.
Don ainihin abin da ya bambanta mu da saura kenan, mu muna cewa addini ya tabbata ne, duk hankoronmu addini ya tabbata ne. To, sawa’un ya tabbata ko bai tabbata ba, hankoron da za mu yi kenan har mu cika. In har ya zama mun cika, ko an kashe mu ko mun mutu, amma dai muna nan kyam a kan sai addini ya tabbata, to mu mun yi nasara.
Amma wani abu da na kan fada, na sha fada cewa, ko da ba wannan lokacin ba amma yana nan wani lokaci zai tabbata. Wannan kiran da muke yi, da ace iyayenmu ne suka fara da mun yi nisa, inda kuma kakanninmu ne suka fara ai da yanzu tuntuni an kafa. To ta yiwu ya faru lokacin ‘ya’yanmu ko jikokinmu, amma dai zai dai tabbatan, saboda Alkawarin Allah ne. Alkawari na Allah ne, Allah kuma baya saba alkawarinsa.
Wannan shine tayama Sahibul Asr Wazzaman (AS), domin ana shimfida ‘ardiyya’ ne na bayyanarsa. In abin ya zo ne ba zai zo ne ya samu shantakakku, sai su ne za su zo su zama gwaraza a lokacinsa ba.
Mu kaddara akwai shantakakku wadanda za su fara (bayan bayyanar nasa), amma (zai zama) akwai wadanda ‘already’ sun riga sun farka suna tsaye kyam, kuna tsammanin su wane ne za su fara zabura? Kuna tsammanin shantakakku ne za su ce ah, ka bayyana ne? Ai shikenan yanzu za mu fara gwagwarmaya?
Ina! Ai za su fara tsurori ne; anya kuwa kai ne Mahdin? Ai Mahdin mu ba a ce mana zai zo haka ba; anya kuwa ai to yanzu dai a dan saurara saboda ana sanyi; to a dakata tukunna saboda ka ga yanzu al’amura na da wahala sai mun dan samu abin tabawa. Sai sun rika kawo tsurori, tsurori guda dubu da daya, duk sai sun kawo na cewa ba za a yi ba, a lokacin bayyanarsa. Karshen al’amarin kila sai Imam din ya shiga girban wuyayensu, wasu ma ba za su bi bane sam.
Ta yiwu wanda ba shantakakke bane shine zai farka (a lokacin), wanda tun asali ma shi bai san da abin ba, sai ka ga shi ya ma fi wanda shi ya sani amma bai yi komai ba. Kar ka sha mamakin wanda tun asali bai ma sani ba, bashi da labarin bayyanar Sahibul Asr Wazzaman (AS), bai ma san shi ba, amma sai aka ce ya bayyana, sai ya ga gaskiya, sai ya amsa. Wani kuma yana jiransa ne, amma ba aikinsa yake ba, sai yace ba shi bane.
Don haka ne aka ce zai zo ma wasu za su ce anya kuwa shine? Aka ce ai saboda wadanda ake tsammanin su ne alamomin addinin wasu su ne zai girbe wuyayensu, irin wadanda suke cewa sune a kan tafarkinsa alhali kuma sun danne mutane ne, suna jiransa amma suna nan tare da mahukuntan da suke sabanin addini. To kuma ko ya zo din suna nan tare da mahukunta din ne, to a lokacin kuma za su ce za su balle (daga binsa ne) ma.
(Don haka), ya zama wannan hadafin ya zama yana nan, akwai hadafi (shine burin tabbatan addini), akan shi kuma ake komai da komai, kowane bangare yana kamawa yana ba da nasa gudummawar.”
— Shaikh Ibraheem Zakzaky a yayin ganawarsa da wakilan Dandalin Matasan Harkar Musulunci, ranar Talata 11/01/2022 a gidansa da ke Abuja. Saifullahi M. Kabir ya rubuto daga audio din.
📝Dan Fudiyya

Tags:
Jagoran Gaskiya