Ta Yaya Zantuba Daga Kallon Firm Ɗin Batsa (Blue firm)



YAYA ZAKA TUBA DAGA KALLON FILM NA BATSA......


Amsa a Dunkule.


Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga sabon komai nisan kuwa da ya yi to wannan lamarin ne babba. Kuma duk wanda ya samu kansa a wannan halin to ya yi kokarin karfafa wannan azamar tasa sosai don cimma wannan nasarar.

Marhalolin da zai kai ga cin nasarar yin mubaraza da sabonsa zamu yi nuni da wasu abubuwa da suka hada da:

1. Lura da abubuwan cutarwa da sabo yake da shi

2. Duba mutuncin kansa

3. Duba girman Allah madaukaki da kiyaye umarninsa

4. Duba kimar da take cikin tsarkake rai wurin gaba da sabo da son rai wanda yake wani lamari ne na cin nasarar rai.


Sannan kuma duk sai ya cike lokacin da ba ya komai da duba litattafai, motsa jiki, hardar Kur'ani, ibada, azumi da sauranibadoji don neman kusanci da Allah. Da watsar da duk wani abu da yake iya jawo masa yin sabon.

Babbar lamari a nan shi ne ka da mutum ya yanke kauna daga samun rahamar Allah ko barin dogaro da shi. Don haka ka da mu sake mu samu yin sanyi wurin yin tuba, don haka sai mu tashi mu yi mubaraza da yin sabo tare da kiyaye abubuwan da muka yi nuni da su a sama. Idan muka neman taimakon Allah da tausayinsa ne zai taimaka mana cikin samun nasarar wannan lamarin.


Mu lura cewa fahimtar munin kallon wannan batsar kawai wani irin farkawa ce da da tausayawar Allah gare ka, kuma kokarin da kake yi na ganin ka bar wannan kallon shi ma wani kokari ne da rai take yi don cin galaba kan rai da munanan ayyukanta wanda yake nuni da kama hanyar tuba ga mutum wanda yake lamari mai kima matukar gaske.  


 Imam Sadik (a.s) yana cewa: Aljanna an cakuda ta da wahala ne, amma wuta kuwa an cakuda ta da abubuwan jin dadin rai ne.


A nan zamu yi nuni da wasu lamurra masu sanya karfafa niyya da azama ga mutum mai son barin yin sabo kamar haka


Amma dole ne mu sani cewa tuba tana da wasu marhaloli kamar haka:


Niyyar barin sabo


Barin sabo


Gyara halaye (maye gurbin munana da kyawawan halaye).


Idan baka yi aure ba sai ya yi saurin yin aure domin biyan bukatar sa ta hanyar halal domin samun abin da zai taimaka masa kawar da duk wani sabo.

Abokina ka sani yakar sabo yana tare da waswasin shedan da yawa, sai dai yana da matukar kima da jin dadin cin nasara kan shedan. Don haka ka yi kokari matuka ka karfafi azamarka ta barin sabo, kuma a kowane hali ne kake kana da wani karfi mai taimako shi ne Allah madaukaki mai tausayi da jin kai, don haka sai ka dogara gaer shi ka nemi taimakonsa.

Ka da ka yanke kauna daga rahamar Allah a kan wannan tafarkin, ka nemi taimakonsa ka dogara gare shi, zai taimaka maka in Allah ya so.......🌹


©Ahmad wulaya ✍️🌹


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/


DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post