@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Bismillahir-rahmanirrahim....✍️
Banyi tsammanin da'akwai wani mutum anan duniya da zaice "Shi bai damu da mutane su soshi ba,"Kai! har fada zakaji masu hankali na yiwa saurayi ko budurwar da'aka ce ana qaunarta ta wulaqanta wanda ya fadi hakan.
Mu sani burin kowane mai rai shine,duk wurin da yaje a karbe shi hannu bibbiyu babu tsangwama bare nuna bambanci,idan da zaka tara dukkan matasan da ke duniya,ka tambayesu me sukafi so aduniya? Za su baka amsa gaba dayansu da cewa,"Suna son suyi suna"(wato su daukaka).Idan kuwa har wani daga cikinsu yace,A'a to lallai son ransa ne kawai.
A bune sananne ga kowa,kowane mutum ya fi son ya ga Al'umma suna neman taimakonsa,idan kuma har yazama da akwai kishiyar wannan aran mutum,to kuwa wannan mutumin zai zama shi mai nema agun mutane ne,ko kuma ya zama cikin damuwa da taqura idan baya son taimakawa jama'a,a lokacinda mutane suka nemi taimakonsa.
Dan'uwa idan bazaka iya ba,to kayi musu kalamai masu kyau,banda qarya da alkawarin da ba za'acika ba,da kuma yaudara.
Idan kana so kayi suna Cikin al'umma,to yana da kyau ra'ayinka ya dace dana al'ummar da kake ciki,kada ka zama mai kyamar al'umma ko hantararsu,kuma kada ka tsani kowa, ka zamto mai qaunar jama'a sai jama'a su qaunace ka, Amma mu sani da akwai wata halayya ta 'Dan'Adam idan ya ce baya qaunarka to ko me zakayi masa bazai burgeshi ba ballantana ya saduda,amma yana da kyau ka hakura ka nuna masa cewa kana qaunarsa.
Mutum ya kan gamu da wani akan hanya ko mu'amala ta hada shi da shi sai kaji baka kaunarsa, ka tsane shi,To 'Yan'uwa yana da kyau kada ka nuna masa tsangwama.
TO MENE NE ABINYI ?!
.
Yana da kyau ka kusanceshi,ka kuma zauna dashi ka saurari ra'ayinsa akan rayuwa,Sai ka samu a wani bangaren kunyi tarayya amma idan ka tsaya nesa dashi, Kaki kusantarsa to kullum sai wutar gaba da shi ta yi ta ruruwa,ba tare da kasan daliliba.
Akwai hanyoyin da idan ka bisu zaka zama kayi suna acikin al'umma ko da ka kasance marar son shiga cikin jama'a da rashin yin magana da kuma kamun kai, Ka zama mai sauqin kai da iya mu'amala da Jama'a Domin sai idan mutane basa sonka ne suke tsangwamarka, Lallai baza kaji dadiba in hakan ta kasance kuma hakan zai saka cikin damuwa, kuma mun san illolin da take haifarwa ga lafiyar 'Dan'adam.
A lokacin da mutum yake ganiyar aiki(ko ya samu wani matsayi) Zaka tarar jama'a na barkowa ta ko'ina, Wadansu na zuwa neman alfarma, Wadansu kuma maula da taimako, Wadansu kuma suna zuwane don neman suna.
To amma ka sani dan jama'a sun zamanto masu qaunarka to ba zai yiwu ace abin hannunka kawai kake amfani dashi domin jawo su a jikinka ba, Musani cewa Matsayi, Dukiyarmu ba itace ke sa jama'a zuwa inda mukeba, Hadi da kyawawan halayenmu,To dan haka mu nemi soyayyar mutane ta hanyar kyawawan dabi'unmu ba'abinda muka mallaka ba, kyakkyawar mu'amala da mutane itace jigon soyayya, kuma zuciya na kyamar abu dalilin mummunar aiki wajen mu'amala.
Na'am, Idan mutum ya zama mai sauqin kai, to lallai jama'a za su dinga rabarsa ba tare da Shakka ko kokwanto ba, Mutane suna lurane da irin yadda ka daukesu da irin yadda ka'aje su, Idan zaka dinga ajiye kowanne mutum a iyakarsa kana mai qasqantar da kai da kawar da kai ga tinanin don me zan yi mu'amala dashi, to sai kaga kana mu'amala da bangarori daban-daban wadanda suka sha bamban kan ra'ayinsu da abinda suka mallaka.
Allah Yasa Mudace....