~Sheikh Ibraheem El'Zakzaky (H)
su mutane sun dauka nasara shine kafa daula. Idan kafa daula it ace nasara, to da yawan Annabawa ba su yi nasara ba, don basu kafa daula ba.
Annabawa nawa suka kafa daula? Har uban Annabawa, Annabi Ibraheem (AS) bai kafa daula ba. Daga cikin Ulul-Azmi, kamar yadda Manzon Allah (S) yake cewa, su biyu ne kawai daga cikin Ulul-Azmi suka zo da ‘tusaif’; Shi da Annabi Nuhu.
Shi Annabi ya yi dauriya, bayan an yi gwaji ya kai intaha sai da ya roki Allah yace ya Rabbi wannan gwajin kar mutane su kafirce. Don ance musu za a kawo faraj, da suka zo suna tsammanin wa’adin faraj din ya zo sai aka ce saura shekara goma. Sai rabin mutane suka yi ridda. Sai aka sha wahala, bayan shekara goma aka ce faraj zai zo. Da aka zo shekara goma aka ce ba faraj a yanzu sai shekara 10, sai kasha biyu cikin ukun wadanda suka rage suka tafi.
Sai aka sake cewa faraj sai shekara 10, wasu suka kara tafiya. Sai da aka zama saura ‘yan kwarori, sannan da aka sake cewa faraj sai shekara 10, shine Annabi Nuhu ya shiga magiya, yana kuka, yana cewa ya Rabbi ba wanda zai yi imani kuma. To shine aka tsamatar da shi da mutum 84, su kwarori. Da an sake jarabawa da kila cikin 84 din 80 su tafi su bar hudu. In jarabawa tai jarabawa haka ke aukuwa. To sai ya shiga magiya, sannan aka kawo mafita. To, shi ya kafa daula.
~Sheikh Ibraheem El'Zakzaky (H) yayin jawabin rufe mu'utamar din sisters a zaria Ranar 20/09/2015
Rubutawa.........✍️ Matashi Ɗan Gwagwarmaya Ibraheem Sani Fudiyyah Yankara
Daga Zauren Tafseer Da Hawaban Jagora
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com