Cewar Sheikh Yaƙub Yahaya Katsina.
Daga Hassan Abubakar Ahmad Ɗan Sister Katsina.
Manzon Allah (S.a.w) yana cewa; "kuso Allah (Swt) da ni'imomin da yake ciyar daku" ya baibayeku da ni'imomi kala-kala. Sannan ku soni saboda son da Allah yakeyi mani. Sannan Manzon Allah (S.a.w) ya umarcemu da mu Tarbiyyartar da 'ya'yanmu, Son Al'kur'ani, karatun Al'kur'ani, son 'ya'yansa, dashi kansa Annabin. Wannan umarce-umarce ne daban-daban, a wurare daban-daban a mu halli daban-daban.
A irin wannan Rana ta Mauludin Manzon Allah (S.a.w) Wani nau'ine na nuna wilaya, da soyayya ga Manzon Allah (S.a.w), da irin wannan salo na bukukuwa. Biki ko shagali, ko Wani abu mai kama da haka. Ɗabi'a ne a cikin ɗan Adam saboda ɗan Adam, tun a salin haliltar sa, Allah (Swt) ya halilceshi da nuna farin ciki a lokacin farin ciki, da nuna damuwa a lokacin damuwa.
Kuma ko wacce Al'umma a kwai hanyar ta da take bi tana nuna farin cikin ta, da murnar ta, a kwai kuma bukukuwa daban-daban. Ko da Musulunci yazo Manzon Allah (S.a.w) ya iske Mutane suna bukukuwa daban-daban, suna nuna murna daban-daban, ta fuskancin da ya shafi haihuwa ne, ko abun da ya shafi aure ne, ko abun da ya shafi zagayowar Shekera a kan wani abu, sai Musulunci ya yi ma abun ƙwasƙwarima a ka ɗorashi a kan dai-dai.
Bukukuwa ko a nan inda muka samu kan mu, zamu ga cewa, a kwai bukukuwa daban-daban da Mutanen daban-daban suke ta'tayi. Ina faɗin wannan maganar ne, saboda a gurin waɗan su, Mutane waɗannan bukukuwan a gurin su, kamar wani bakon abu ne, ko nace suna: kallon shi, a matsayin 'Haramun" bidi'a ko wani abu mai kama da haka. A halin suna'nan sunaji suna gani ba bikin da ba ayi. A yau muna Asabar 08/October/2022 M. To Ranar ɗaya ga watan anyi bikin kirkiro Nijeriya. Wanda kuma manya duka, sun yi tarayya a cikin wannan biki, har da ma masu Addini.
Har da malamai, har dawasu ma sun taka fareti, da sunan ƙungiyar su, ta Addini. Amma Bai taɓa zama matsala ba, tare da cewa, ita Kasar an ƙirƙireta ba tare da Addini Ba, ba an kirkireta ba saboda Musulmi, bama a ƙirƙireta ba saboda da ƴan ƙasa ɗin ba. Waɗanda Suka ƙirkƙieta sun ƙirƙiri ƙsar ne saboda buƙatar kansu kawai. Amma a haka zakaga cewa, anyi irin waɗannan bukukuwa anyi tarayya, sunyi Murna, amma Bai taɓa zama matsala ba. Abun da ke matsala nuna murna, da Farin ciki da haihuwar Manzon Allah (S.a.w) shi ne Kawai matsala.
To, da yake al'amrin na Allah (Swt) ne, a kwai hannun Allah (Swt) a ciki abun, ba, baya yakeyi ba gaba yake ƙarawa. Kuma insha Allahu Ta'ala Wani nau'ine na salo insha Allahu ga Maulud Manzon Allah (S.a.w) ne za a samu (Sauyi a kasar nan insha Allah) ina tsammanin babu wanda bai gaji da halin da ake cikin ba. Ina tsammanin babu wanda bayason a samu Sauyi, tunda a gwada tsarinrika daban-daban to, a gwada na Annabi Muhammad (S.a.w) mana. Na'am nasan su ba zasu ce, a zo a gwada na Annabi ba. To, amma mu mun kama hanya... Kuma insha Allahu Ta'ala ga Maulud Manzon Allah (S.a.w) ne a wannan kasar za a samu Sauyi.
_____Malam Yaƙub Yahaya Katsina State ya yi wannan jawabin ne ya yin rufe muzaharar Mauludin fiyyayan haliltar Muhammad (S.a.w) da ta guda a cikin jahar katsina.
@MediaforumKatsina
(#0018)
13/Rabi'u Awwal/1444 H.
09/October/20222 M.
Update 08/Nov/2022 M.