@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE
Tohm Soyayya dai ta zama dole, kuma babu soyayyar da ta zama {'Dahir}, kamar Soyayya saboda Allah. Shi yasa ma musulunci ya koyar damu zama masu gaskiya da yin so domin Allah, da kuma Qi domin Allah, Addinin Musulunci ya koyar damu cewa Namiji da Mace zasu iya kulla kyakkyawar alaqa da ta kafu akan aure.
Dan haka Idan har ka tabbata ba yaudara da batamata lokaci zakayi ba, da gaske kake sonta kuma zaka aureta,to abinda farko ya kamata kafara yi shine ; Kasan wacece ita?
Ana son kafin ka nemi soyayyar mace ka fara sanin wacece ita...?
Ka tabbatar cewa wacce zaka fara soyayya da ita, mai Addini da tsoron Allah, da kuma Tarbiyya, Ilimi, Nasaba, Mai shigar Mutunci da kamala ce. In ko akasin haka ne to ka kauce mata {Ma'ana} Karka aureta. Domin rashin tarbiyya mai kyau ga 'ya Mace yana rusa iyali.
Sannan Abu na biyu bayan ka gama sanin wacece ita,Ka kuma aminta da Tarbiyyar ta, To kai tsaye ka bayya na mata soyayyar ka da kanka.
In Allah Ya yadda, Kamar yadda ka gina niyyar ka mai kyau to haka zaka yi nasara kuma zaka gina soyyarka da kyau.
Idan kana son fara Soyayya da mace to kada kaji shakkar komai ka fada mata kana son ta. Amsar daya ce cikin biyu, "Eh" ko "A'a".
Dan haka da kanka ka tunkari gidansu, kasa anema maka izinin magana da ita daga Mahaifanta, ko danginta, bayan ka samu izinin magana da ita, to ananne zaka fada mata mike cikin zuciyar ka. Bayan ka yi nasarar bayyana mata abinda ke ranka, sai ka Dan bata lokaci tayi tinani, Idan har ka samu amincewa agareta tohm Alhmdullh, na tayaka Murna.
Idan ko bata amince ba, to ni shawara ta Anan shine kawai ka haqura Karka matsa mata kaje ka nemi wata,Karka karaya, Insha Allahu zaka samu wacce take sonka, ba dika akataru aka zama daya ba, Idan ko Allah ya qaddara matarkace to da kanta zata dawo gareka, Matar mutum kabarinsa.
JAN HANKALI NA A GAREKA SHINE;
Idan za kazo wurin mace farkon haduwarku, Ka kyautata shigarka, Ka zama mai kamun kai, Ka nutsuw, Ka san me zai rinqa fitowa daga bakinka, Ka kuma fahimci kalamanta da yanayinta, dan Kasan irin zaman da zakai da ita.
Aqarshe bayan kayi nasara Ina so kasani shi so tamkar fure ne, dole anayi anamar bayi, ta hanyar kyautatawa da kulawa.Wannane zai dauwamar da soyayyarka a Zuciyarta har abada. Allah Ya tai make ka.