Shugabancin Wannan Al'umma Bai Cancanci Matsoraci Kuma Makwadaici Ba. Shaikh Ibraheem Zakzaky (h)




_______Sheikh Ibraheem El'Zakzaky (H)_____________

Qoro wani mataki ne na rowa. Da rowa da kwadayi tare suke tafiya. Abokanan juna ne. Duk lokacin da ka ga marowaci za ka ganshi makwadaici. In kuma ka ganshi makwadaici, za ka ganshi marowaci ne. Shi yasa ma wani lokaci ake kiransu abu guda. Kamar a wani huduba na Amirulmuminin, yace; “Kun san kuma ba yadda za a yi a ba da amanan al’umma ga marowaci.” To, amma makwadaici yake nufi.

Yana cewa ne: “Shugabancin wannan al’ummar bai cancanci matsoraci kuma makwadaici ba. yana bukatar jarumi ne wanda bashi da kwadayi.” To, bai ce makwadaici ba, sai yace marowaci shi, don haka ma da na zo karantawa sai nace marowaci a nan yana nufin makwadaici, domin al’adar marowaci ne kwadayi. Mai kwadayi na kwadayin abin hannun mutane, kuma shi baya bayarwa. Sai aka ce kawai baya bayarwa (marowaci).

A takaice, shi rikon al’umma dai bai cancanci masu siffa irin wadannan ba. Akwai kari ma, yace ‘Kun san kuma rikon wannan al’umma bai cancanci jahili, matsoraci kuma makwadaici ba.’ A lokacin nace yana nufin wane ne, wanda aka ba shugabanci, shi ke da wadannan siffofin. Ko ma su wane da wane, da ma wane. Su suke da wadannan siffofin.

-- Sheikh Ibraheem El'Zakzaky (H) a yayin Jawabin rufe mu'utar din sisters a Zaria, Ranar 20/09/2015

Ibraheem Sani Fudiyyah Yankara  (Khadeemu Ahlul Baety)

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post