SHIRIYAR AL'UMMA TA DOGARA NE DA GYARUWAR 'YAN KADAN!_ Shaikh Ibraheem Zakzaky (h)




-----EMSANEE----- 

Ya zamo cikin al'umma kamar yadda yazo a Al-qur'ani 'Waltakum minkum Ummatun, yad'una ilal khayri wa ya'amaruna bil ma'aruf wa yanhauna anil munkar'. Kaga ance 'Minkum Umma' Alhali Kuma gaba daya duk cikinku Ummah ne. Ummah faffada, Al'ummar Musulmi. To kuma sai akace; a sami wata Ummah din a sami wani yanki kuma. "Su kuma suna kira ga Alheri suna hani ga mummuna wato suna umarni da mai kyau suna hani ga mummuna.

Allah (T) yace:- Wadannan sune masu samun nasara. Wannan ya nuna kenan a cikin Ummah din akwai wata Ummah wannan Ummah gaba dayanta. Wannan Ummah Taf'diliyya' Minkum. Su kuma wadansu kalilan, wanda suka ce; to ku zamu kira sauran ya zuwa alheri da umurtar su da mai kyau da hanasu mummuna.

Wato a takaice a dunkule kokarin muga mun dawo dasu, mun tabbatar dasu a kan tafarkin addinin a kowane lokaci. To, wannan idan akwai dawainiyya data hau kan Al'umma gaba daya, to ita kuma wannan Al'ummah mai da'awa, ita kuma wani abu daban ya sake hawa kanta.

Ainihin gyaruwar al'ummar da shiriyar Al'ummar ya dogara ga wadannan kadan din ne. Idan kadan din nan aka neme su aka rasa, to Al'ummar zasu lalace. Idan kadan din nan sukayi aiki dan kadan, to al'umma zata gyaru dan kadan. Idan kadan dinan suka gyaru sosai, sukayi kuma gyara sosai, za'a ga Al'umma ta gyaru sosai.

Don haka ke nan, kaga ita wannan al'ummar kebantacciya, to akwai wani karin alhaki a kanta, baya ga alhakin daya hau kan al'ummar gaba daya kenan. Ya hau kan ita wannan Al'umma ta zama samfuri. Al'ummar 'Da'iya' (mai da'awa), ta zama samfuri, ya zama cewa kowanne alamine na abin da yake fadi. Wato shi wannan abin da yake cewa ayi, shima yana yi. Abin da yace a bari, shi kuma ba yayi.

—Jagora Allamah Sayyad Zakzaky (H) a wani Jawabinsa daya gabatar a Shelarun Baya.

Allah ka faranta ranmu da samun yancin jagoranmu Allah Bamu Da Wani Gata Sai Naka Kaine Komai Namu Ya Allah hukuncin ka kawai muke jira ba nasu ba.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post