Sheikh Al-Zakzaky ya bani Muhimmin sako ga yan Kannywood - Inji Ali Atwork




Jarumin barkwanci a Kannywood, Aliyu Muhammad Idris, wanda aka fi sani da Ali Artwork ko kuma Maɗagwal, ya bayyana cewa akwai muhimmin saƙo da jagoran Shi’a a Nijeriya, Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky, ya ba shi domin ya isar ga ‘yan fim ɗin Hausa.

Amma ya ƙaryata masu cewa ya zama ɗan Shi’a, wai don haka ne ma ya kai ziyara ga shahararren malamin a gidan sa da ke Abuja.

Da ya ke zantawa da mujallar Fim, Ali Artwork ya ce, “Masu yaɗa cewa wai na karɓi Shi’a ƙarya su ke yi. Duk wanda ya san ni, ya san cewa a kowace ɗariƙa ina da mutane. Da ma na saba ziyartar malamai tun ba yanzu ba, irin malaman Izala, Tijjaniyya, Ƙadiriyya da duk wani malami, duba da yanayin sana’a ta na nishaɗantarwa, kowane ɓangare na al’umma su na ji, kuma su na kallo. 

“Sannan a dukkan mutane su na so kuma su na sha’awar abin da na ke yi. Kuma su kan su su na so in zo mu ƙulla mu’amala ko na kasuwanci ko kuma wani abu mai kyau haka. Don haka zuwa na ba wani sabon abu ba ne.”

Maɗagwal ya yi nuni da cewa shi mutum ne wanda ke kai wa malamai na bangarori daban-daban ziyara.

Ya ce: “A baya na ziyarci Sheikh Ahmad Gumi, duk da mun je ɗaukar hira da shi ne a kan abin da ya shafi harkar zakka da waƙafi. 


“Sannan na ziyarci ɗan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, mun yi maganganu da shi. 


“Haka shi ma Sheikh El-Zakzaky mun ziyarce shi ne don mu sada zumunci, kuma mu yi masa jajen abin da ya faru da shi, da sauran su. Wannan shi ne.”


Ali ya ci gaba da cewa, “A cikin mutanen sa akwai masoya na, kuma su na kallon abin da na ke yi na nishaɗi da sauran su. Waɗannan su ne maƙasudin zuwan namu.”


A kan yadda ganawar tasu ta kasance, jarumin ya ce: “Mun ji daɗin tattaunawa da Malam. Ya sanar da mu wasu abubuwa na rayuwa waɗanda ba mu sani ba. Haka kuma ya ba mu shawarwari a kan sana’ar mu da kuma yadda mutane su ke kallon mu a matsayin waɗanda su ke ɓata tarbiyya.


“Malam ya ce gaskiya wannan abu ne wanda bai kamata ba, wannan harka ce da za a iya amfani da ita wurin tura saƙo, mu yi abu mai kyau, kada mu yi abin da zai taɓa ƙima da mutuncin addinin mu, mu rinƙa nuna wa mutane yadda za su yi rayuwa mai kyau, in kuma mun nuna wani abu wanda mara kyau ne, to a ƙarshe menene darasin da ake so a nuna. ‘Akwai ilimi a harkar naku sosai’.


“Malam ya ba mu shawarwari, kuma ya nuna mana irin sukar da ake yi mana a kan harkar duk ba haka ba ne. 


“Sannan ya faɗa mana wasu abubuwa da za mu riƙa amfani da su wurin wayar wa da mutane kai, tunda abin da mu ke yi abu ne mai tarihin gaske.


wani fim a kan Ɗanfodiyo, wanda a lokacin har sun nemi shawarar Sultan na Sokoto da sauran su, amma abin ya turje, aka ƙi barin fim ɗin ya fita, da sauran su. 

“Wannan shi ne abin da mu ka ɗan tattauna kenan a taƙaice. Bayan shi babu wani abu da mu ka tattauna. 

“Ya kuma ce a sanar da ‘yan’uwa ‘yan fim ga saƙon da ya bayar a faɗa masu.”

Bayan mun kammala, mu ka yi sallar isha’i, aka yi addu’o’i.

“Waɗanda mu ka je da su sun haɗa da AGM Bashir, Usman Madobi, Nura Shugaba, Ahmad M. Kubau da kuma mawaƙiya Ummi Kano.”

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post