@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KADA KI BIYEWA A'ISHA WACCE KE NUNA JI-JI-DA-KAI GANIN ANNABI YA FI SONTA
Shi Qur'ani ko Hadisi bai taba zuwa da wani abu ba face umarni ko hani ko kuma labari don a dau darasi daga ciki. Da ba don wadannan abubuwa uku ba haqiqa da ba a saukar da Qur'ani ba, in kuwa aka saukar zai zama babu ma'ana cikinsa.
Wadannan mata biyu da muka ambata a sama mata ne na Annabi Muhammad (S. A. W. W) kuma iyaye ga dukkan wani mumini ko mumina. Saboda haka ya kamata ace sun samar da kyakkyawan abin koyi ga 'ya'yansu a matsayinsu na makarantar farko gare su.
Sanin wannan da Umar yayi kuma yaga wasu abubuwa na fitowa daga gare su wadanda basu dace ba sai ya dau mataki na kawo gyara ga 'yarsa a matsayinta wacce ya isa da ita don gudun kada mummunan abin koyi ga 'ya'yan nasu.
Qur'ani ya kawo bisa zargin da yake musu (A'isha da Hafsat) na hada kai da taimakon juna don cutar da Manzon Allah (S. A. W. W) har ta kai ya qaurace musu na tsahon wata guda a masallaci.
Inda Allah (T) ke cewa :
"KUMA IDAN KUKA TAIMAKI JUNA A KANSA (wajen cutarwa), TO, LALLE ALLAH SHINE MAJIBINCINSA DA JIBRILU DA KUMA SALIHIN MUMINI (Imam Ali (A. S)....................). "
Ya tabbata lalle a kansu ne wannan aya ta sauka kamar yadda za mu gani cikin wannan riwaya :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
(4914) - حدثنا علي: حدثنا سفيان: حدثنا يحيى بن سعيد قال: سمعت عبيد بن حنين قال: سمعت ابن عباس رضي الله عنهما يقول:
أردت أن أسأل عمر، فقلت: يا أمير المؤمنين، من المرأتان اللتان تظاهرتا على رسول الله صلى الله عليه وسلم؟ فما أتممت كلامي حتى قال: عائشة وحفصة
[89]
Bukhari yace: Aliyu ya bamu labari: Sufyan ya bamu labari : Yahya Bn Sa'eed ya bamu labari yace : " Na ji Ubaidu Bn Hunain yace : Na ji Ibn Abbas (R. A) yana cewa :
" Nayi nufin na tambayi Umar, sai nace : Yaa shugaban muminai, wadanne mata biyu ne wadanda suka hada kansu akan Manzon Allah (S. A. W. W)? Ban gama maganar tawa bama har yace :
" A'ISHATU CE DA HAFSAT. "
(BUKHARI, KITABUL TAFSIR, HADISI MAI LAMBA: 4914)
Wannan abinda ya faru ya batawa Umar rai, domin bai ga hakan ya kyautu gare su ace sun hada kai don cutar da Annabi (S. A. W. W). Saboda haka sai ya tashi da kansa har gidan 'yar tasa Hafsat yana yi mata fada da gargadi don ta gujewa fadawa cikin fushin Allah ta hanyar cutar da Annabi (S. A. W. W. ).
Riwayar tana cewa :
(5218)- حدثنا عبد العزيز بن عبد الله: حدثنا سليمان، عن يحيى، عن عبيد بن حنين، سمع ابن عباس، عن عمر رضي الله عنهم: دخل على حفصة فقال: يا بنية، لا يغرنك هذه التي أعجبها حسنها وحب رسول الله صلى الله عليه وسلم إياها يريد عائشة، فقصصت على رسول الله صلى الله عليه وسلم فتبسم .
Abdul-Azeez Bn Abdullahi ya bamu labari : Sulaiman ya bamu labari, daga Yahya daga Ubaidu Bn Hunain, ya ji Ibn Abbas (R. A) daga Umar ya shiga wajen Hafsat sai yace :
" YAA KE 'YATA ! KADA WANNAN WACCE KYAWUNTA DA KUMA (ganin) SOYAYYAR DA MANZON ALLAH (S. A. W. W) KE NUNA MATA HAR TAKE JI-JI-DA-KAI YA RUDAR DAKE. " SAI (Manzon Allah (S. A. W. W) YAYI MURMUSHI. (da jin wannan abinda Umar ya fada. "
(BUKHARI, KITABUN-NIKAH, BABIN NUNA SOYAYYAR MUTUM GA WATA MATARSA FIYE DA SAURAN, HADISI MAI LAMBA : 5218)
A wata riwayar kuma yake cewa :
............. فقام عمر، فأخذ رداءه مكانه حتى دخل على حفصة فقال لها: يا بنية إنك لتراجعين رسول الله صلى الله عليه وسلم حتى يظل يومه غضبان؟ فقالت حفصة: والله إنا لنراجعه، فقلت: تعلمين أني أحذرك عقوبة الله، وغضب رسوله صلى الله عليه وسلم، يا بنية لا تغرنك هذه التي أعجبها حسنها حب رسول الله صلى الله عليه وسلم إياها، يريد عائشة،.............."
" Sai Umar ya tashi ya dau Bargonsa har ya shiga wajen Hafsatu, sai yace mata :
" Yaa ke 'yata ! Wato ke kina neman (dole) sai Manzon Allah (S. A. W. W) ya juyo kanki (ya fifita ki kan sauran matansa har hakan ke sa) ya wayi gari yana cikin fushi ?" Sai Hafsatu tace :
" Eh, wallani ni ina (neman dole) sai na juyar dashi !" Sai nace :
" Ashe baki san ni ina tsorace miki azabar Allah da kuma fushin Manzon Allah (S. A. W. W) ba ko ? Yaa ke 'yata ! Kada wannan wacce kyawunta yasa Annabi (S. A. W. W) yake sonta (har hakan) yasa take ji-ji-da-kai. " Yana nufin A'isha (in ji Ibn Abbas)....... "
(Bukhari, Kitabul-Tafsir, Babin: kana neman yardar matanka, Hadisi mai lamba : 4913)
DARASI
__________
Tabbas wannan Hadisi na da dimbin darusa wadanda za a iya fitar dasu da dama, amma dai ga kadan daga cikin :
(1)- A matsayin Uba bai kamata ace ya bar wata 'yarsa ta hada kai da wata wajen cutar da mijinsu ba. Dole ya zama yana yi mata fada da kuma nuna mata abinda zai fi zame mata alkhairi.
(2)- Annabi (S. A. W. W) na nuna tsananin soyayyarsa ce da kuma fifita Ummul-Mumunina A'isha akan sauran matansa saboda kyawunta, duk da cewa ya umarce mu da mufi son mace ma'abociyar addini fiye da kowacce irin mace.
(3)- Ummul-Muminina A'isha mai ji-ji-da-kai ce kamar yadda Umar ya shaideta, shi yasa yake gargadi 'yarsa kan cewa kada ta biye mata.
(4)- Annabi (S. A. W. W) mai kawaici, shi yasa da Umar yayi wannan magana bai ce komai ba sai dai murmushin da yayi.
D. S
Da fatan mu iyayen 'ya'ya mata za mu dau darasi daga wannan .
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
26th November, 2022/ 2nd Jimada-Ulah, 1444.