Mu'utamar Na Dandalin Matasa (Yankin Zaria) A Rana Ta Biyu Daga Garin Kudan.



A yau Asabar 19/11/202, yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky(h) na dandalin matasa na yankin Zaria, sun shiga rana ta Biyu a gabatar da mu'utamar a garin Kudan. Mu'utamar din da a shigesa da yammacin jiya Juma'a 18/11/2022.

Alhaji Sani Sabi'u Danja (Alheri Bread), shine ya kasance bako na musamman mai gabatar da jawabi da safiyar yau Asabar, akan maudhu'i mai taken 'Muhimmancin dogaro da kai ga matashi ta  hanyar kasuwanci'. Malamin ya kawo muhimmancin kasuwanci a musulunci domin dogaro da kai musamman ga matasa, da kuma haskawa matasa wasu hanyoyi da dabarbarun kasuwanci. 


—daga faruq Sani Kudan

Ma'asumah Nigeria News update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post