MU MAYAR DA RAYUWAR ANNABI (S) TA ZAMA MADUBINMU

 


— Inji Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). 


Yace: “Wannan lokaci namu na murnar zagayowar haihuwar Manzon Allah (S) lokaci ne na sake duba kawukanmu. Wato mu mai da rayuwar Annabi (S) tamkar madubi, madubin da za ka duba ka ga kanka. In muka dubi rayuwar Annabi da al’ummar da ya kafa ya yi gwargwarmayar da ita, sai muka zo muka dubi kawukanmu yaya muke mu?


“Ka san in ka duba madubi, idan ka sha kwalliya ai kwalliyar za ka gani ko? In kuma baka da kyan gani haka za ka gani. To, mu yanzu ko da muna ganin lafiya lau, to ka kwatanta da madubin Annabi (S), in muka duba Annabi muka dubi kanmu, sai mu ga da wane gwargwado ne muka yi nesa da shi?


“Yanzu da zan ce muku ai idan aka duba al’ummarmu na yanzu, aka duba al’ummar Annabi (S) ai iri daya ne ba bambanci, na san kowa ce min ba haka bane. To, izuwa wane ‘miqidari’ ne muka yi nesa, don mu yo kusa?.. 


“Daidai wannan lokaci sai mu ga cewa mun dago, al’ummarmu ta zama shigen al’ummar Manzon Allah (S), wannan Annabi (S) ya zama shine abin koyinmu, ya zama samfurin abin da za mu iya kwafa a rayuwarmu, kuma shine mafitanmu a Duniyarmu da Lahirarmu.”


— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a jawabinsa na Mauludin Manzon Allah (S) a cikin birnin Zariya a shekarar 2014/1435.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post