Mlm Zakzaky (h) Yana Maganar Tabligh Amma Almajiransa Suna Ji Suna Gani Almizan Tana Neman Durkushewa..!


... Umar Hassan Gololo... 

ALMIZAN ta isar da sakon gwagwarmaya karkashin jagorancin Malam Zakzaky(H) lunguna da sako-sakon Nigeria, birane da kauyuka. 

Idan ALMIZAN tana bikin cikarta wasu shekaru zaka karanta hirarraki da mutane dabam-dabam masu shekaru da yawa zaka ji da yawansu suna cewa ta hanyar ALMIZAN suka fahimci Harkah Islamiyyah. 

Kamar yadda Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi yake cewa mutum daya ya shiriya ta hannunka yafi a baka jajayen rakuma, wani wurin kuma yace yafi a baka dukkan abinda rana take haskawa. 

Wanene zai iya lissafa yawan Ladan da


wadanda suke da hannu wajen ganin fitowar ALMIZAN duk mako? 

Na sha halartar wuraren post khutba a Masallatan Juma'a dabam-dabam a Arewacin Nigeria, Wallahi yadda nake ganin 'Yan-uwa da mutanen gari suke rububin sayen ALMIZAN sai na Kara tabbatar da cewa akwai abubuwa masu fa'idar gaske da suke samu a cikinta. 

Idan kamar 'Yan-uwa ma'abota Mu'amala da social media suna ga ba zasu iya sayen ALMIZAN su karanta ba, na tabbata akwai wadanda idan aka saya aka basu zasu ji dadi. 

Yanzu fa ALMIZAN tana fuskantar jarrabawa fiye da yadda ta fuskanta a lokacin General Abacha, a wancan lokacin wanda aka kama da wiwi sai yafi wanda aka kama da ALMIZAN samun sassauci, amma duk da haka cikin yardar Allahu Ta'ala ta shallake duk wata makida da sharrin Gwamnatin Abacha. 

Yanzu abinda ALMIZAN take fuskanta shine jarrabawar tattalin arziki, wanda na tabbata da 'Yan-uwa zasu muhimmantar da maganar Malam Zakzaky(H) akan isar da sakon gwagwarmaya, lallai da zamu taimaka mata mu ga ta mike ta cigaba da fitowa kamar yadda ta saba.

Sannan muna kira tare da rokon Hukumar gudanarwar ALMIZAN ta fito da wani tsari a tsakanin 'Yan-uwa Almajiran Malam Zakzaky(H) ko da kuwa bin da'irori ne ana fadakar dasu muhimmancinta da kuma neman koda taro da sisi ne daga garesu domin ganin ta cigaba da fitowa kamar yadda ta saba. 

Muna rokon Allahu Ta'ala Ya tashi kafadar ALMIZAN Ya taimaka mata ta dawo cikin hayyacinta Alfarmar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wa sallam.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post