Menene nayin hassada..!

@MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE

  

    Ni banga Amfanin yin hassada  ba. 

Hakika yin Hassada kan wata Falala da Ni'ima da Allah yayi wa 'Dan'adam,Tamkar kana Qalubalantar Allah ne a cikin hukuncin sa.  Idan nayi tambaya Shin Wanene yake bada Wannan falalar ga muminai ?!  Amsar de itace; Allah(swt), To dan me zaka Qalubalanci Ubangiji cikin hukuncin sa,bayan munsan yin hakan babban zunubi ne. Tukunna ma wai shin 

MENENE ITA KANTA HASSADAR, SUWA A KEYI WA HASSADA ???

 Hassada shine Nuna bakin ciki a zuciya game da wata rahama ta ilimi, dukiya, kasuwanci, lafiya, karatu, kyau, Kyawawan halaye, Mulki, Haihuwa, ko wani matsayi da Allah ya daukaka mutum akai. Domin wannan abubuwa suna daga cikin rahamomin Allah masu girma wanda Allah yake badasu ga wasu daga cikin bayinsa, Amma kuma shi mai hassadar Ransa baya so. 

YA AKE GANE MAI HASSADA???

Shi mai hassadar yana da wani mummunar manufa gashi wanda yake yiwa hassadar. Yayin da wani mummunar Abu ya same shi sai shi yaji dadi aransa, Yayinda Alkhairi ya same shi sai yaji bakin ciki,wani har kaga baqin cikinsa ya bayyana a fiskarsa, ko a furucin bakinsa, ko a aikinsa. 

Shide mahassadi a kullum baida wani buri illah yaga kar kayi gaba,har yayi ta maka mummunar fata da nufin bala'i ko Musiba ta auku agareka ko dukiyarka ko ga iyalinka. 

Kamar Yadda Allah ya fada acikin Alqur'ani mai girma, Acikin suratul Tauba(A yata 97) Cewa;BISMILLAHIR-RAHMANIRRAHIIM. 

"WA YA TARABBASU BI KUMUD-DAWA'IR ALAIHIM DA'IRATUS-SAU'I WALLAHU SAMI'UN ALIM".  Ma'ana "KULLUM MAHASSADA SUNA SAURARO SUGA WASU MUSIBA SUN AUKA GA MUMINAI, (Allah yace) A KANSU NE WANNAN MUSIBAN ZASU SAUQA, KUMA HAKIKA ALLAH MAI JINE KUMA MASANI NE GAME DA MUMINAI. 

ABINDA HASSADA KE HAIFARWA

Hassada yana haifar da miyagun ayyuka guda 3, wanda kowanne guda daya yana tabbatar da mutum ya shiga wuta ta har abada,sai dai wanda Allah ya taimaka kafin ya Mutu ya tuba, ya kuma gyara halayensa. Kuma ko wanne yana jawo mummunar qarshe da mutuwar tozarta. 

1, Hassada yana haifar da girman kai mafi muni. 

2, Hassada yana haifar da kiyayya mafi muni.

3, Hassada yana haifar da muna finci na sosai, mutum ya zama babban muna fiki. 

Hassada shine  farkon abinda Aka fara Saba ma Allah(T) dashi a sama da kuma girman kai. Mai wannan laifi kuwa shine kakan Aljanu, Wato(shaidan/Iblis). 

ILLAR YIN HASSADA

Hakika hassada tana rushe sallolin mutum,Hassada tana rushe Azumi koda na shekaru nawa ne. Hassada tana rushe ladan aikin hajji da umara koda na shekaru nawa ne. Hassada tana rushe ladan  gina masallatai da makarantai, koda guda nawa ne.

Kamar Yadda Manzo (SAW) yace; "Hassada tana cinye Kyawawan ayyuka na mutum, kamar yadda wuta take cinye kirare busassu". 

Sannan raanar tashin kiyama, Mala'ika zaizo,  ya kama shi mai hassadar acikin taron qiyama, Mala'ika zai dakko sarqa ta wuta ya rataya masa a wiya, Sai ya shigar da sarkar ta cikin bakinsa, sannan sai ya fitar da ita ta cikin duburarsa, sannan sai mala'aka yayi masa daurin goro, Sai Mala'ika yayi shela cewa; "Ya ku taron mutane jinni wal insu wannan shine sakamakon mai hassada, Dan haka duk wanda ya Mutu yana Hassada a duniya haka Za'ayi, masa kamar yadda akaiwa wannan mutumin da kuke gani. 

Ranar lahira za'a hada mai hassadar da shaidan ayi musu daurin goro asanyasu cikin akwati a jefasu a cikin wuta ta 6. 

JAN HANKALI GA MAI HASSADA 

Ya ku mahassada, Ku Sani fa dik wanda Ubangiji Allah ya daukaka a wannan duniya ko wanne irin daukaka to babu wani mahaluqin da ya isa ya kasqantar da wannan mutumin. Domin shi Allah mai yin yadda yaso,  kan wanda yaso,  a inda Yaso, ko ana so ko ba'a so ne. 

'Dan'uwa wannan da kake yiwa hassadafa a kullum gaba-gaba yake, kai kuma kana asarar addininka a kullum, ba kuma zaka samu biyar buqataba har abada. Kullum zuciyarka na cikin qunci da bala'i, Karshe kuma ga wutar jahannama nan na jiranka. Dan haka mu guji yiwa  juna hassada bisa rahamomin da Allah ya basu. 

Allah Yasa mudace.



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post