Me ke jawo yawan samun kiyayyar juna ga Ma'aurata

By Fatima Adamu Tinja


ME KE JANYO FARUWAR HAKAN ???!!! 


       Kafin aure kuna soyayya kamar a hadiye juna, Amma da zarar anyi aure wata daya,ko biyu, a yayi yawa wata Uku, Anfara samun matsala wasu har ta kaisu ga saki. Shin me yake janyo hakan ne ??? 

Fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAWA) ya bayyana cewa; "duk mai son ya samu kwanciyar hankali a aure to ya auri mai addini tarbiya, mai hali mai kyau saboda mata masu addinni su ne nasiha ke tasiri a kansu; Shi kuma namiji mai addini ko da soyayya ta kare to zai ji tausayin mace saboda tsoron da yake yi wa Allah.

Masana kan Zamantakewa da halayyar Dan Adam sun bayyana cewa yawan samun kiyayya ga ma'aurata bayan aure ya samo asali ne daga canji da dalilai kamar haka:

KWADAYIN IYAYE

A yanzu yawancin iyaye idanunsu sun rufe da kwadayi da son abin duniya.

Hakan ya sa ba sa bincike a kan wanda za su bai wa  auren ’yarsu, in dai yana da kudi to shi ke nan ba ruwansu da dabi’unsa, kamalarsa, ko cancantarsa.

KARANCIN ILIMI A KAN AURE

Akwai kuma karancin ilimi a kan auren da kuma rashin sanin darajarshi.

Yawancin masu aure ba su dauke shi a bakin komai ba, domin a tunaninsu in dai suna da kudi za su iya yin abin da suke so, su auri mata ko nawa ne.

Sannan rashin samun fadakarwa a kan zamantakewar aure shi ma illa ce babba, saboda wasu auren kawai suke yi, ba tare da sun san yadda ake zaman auren ba.Kawai aboki ya yi, shi ma dole sai ya yi.

GAZAWA DA BIYAN BUKATUN JUNA

Akwai kuma gazawa da biyan bukatun juna da nuna so kamar yadda ake a waje bayan an yi aure.

Idan miji ba ya iya biya wa matarsa bukatunta da kuma sauke hakkokinta a kanshi, hakan zai haifar da rashin jituwa a tsakaninsu da kuma rashin nuna soyayya kamar a farko.

DAUKAR SURUTU DA JITA-JITAR MUTANE

Idan kuma ma’aurata na biye wa surutan mutane da jita-jita, hakika aurensu ba zai dade ba, musamman idan suna boye sirri ga junansu. Ko kuma su rika fadar matsalar cikin gidansu ga kawayensu ko wasu a waje. 

RASHIN HAKURI A TSAKANIN MA’AURATA

Rashin hakuri a tsakanin ma’aurata yakan kawo rashin fahimtar juna, rashin yi wa juna uzuri da kuma saurin mutuwar aure.

KARYA KAFIN AURE

Sannan yi wa juna karya kafin aure yana kawo mutuwar Soyayya Wanda zai haifar da mutuwar aure. Wasu mazan za su iya yin komai don su mallaki mace, su yi mata karyar arziki duk saboda su samu su aure ta.

Idan kuma mace ta je gidansa bayan aure ta ga ba hakan ba ne sai a dinga samun sabani, daga nan za a iya samun matsala da za ta iya kaiwa ga rabuwar aure.

MATSA WA ’YA’YA SU FITAR DA MIJI

Matsa wa ’ya’ya mata a kan su fitar da mijin aure zai iya sa su tsaida wanda bai dace ba; Daga karshe a rika samun, matsala a auren su.

Daga karshe Shawarwari ga ma'aurata shine; Gina Soyayya ta gaskiya, Bincike kafin aure, Hakuri da juna bayan aure,Yawan bada Uzuri musamman ga halayen Mata saboda raunin su, Da sauran su.

Ya Allah ka  dauwamar Mana da zaman lafiya da Soyayya a cikin gidajen mu na aure.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com



1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post