_____________________________
fatimaboutique.fh@gmail.com
______________________________
Da yammacin yau Juma'a ne yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky (H) na dandamalin Matasa a garin Shinkafi Jihar Zamfara suka gabatar da Mauludeen Fiyayyen halitta Manzon Allah Muhammad Bn Abdullahi (S) wanda suka saba shiryawa a duk shekara.
Mauludeen ya gudana ne karkashin wakilcin Malam Yahaya Isa (Wakilin Yan uwa na dandamalin Matasa)
Malam Qaseem Shehu Shinkafi (Wakilin Yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Ya'aqoub Zakzaky) na garin na Shinkafi shi ne Babban Bako Mai jawabi a wannan zama Mai albarka.
Malam Qaseem Shehu Shinkafi a wani bangaren jawabinsa ya Kore shubuhar da ake bayyanawa a matsayin mu'ujizar Manzon Allah cewa "Manzon bai iya rubutu ba" Malamin ya bayyana cewa wannan nakasta matsayi ne da darajar Manzon Allah. "Manzon Allah ya iya rubutu Kuma ya iya karatu Kuma babu wani mahaluki da ya koya mashi,sulhun Hudaibiyyah ya tabbatar da wannan" Inji Malam Qaseem Shehu.
Photo Credit: Fateema Boutique