SHAFE-SHAFE GA YAR UWA:-Duk yanda kike sai namiji ya nemi akasin haka a jikin wata. Misali idan kyakkyawa kike sai yaje neman mummuna, idan fara kike baka zata bashi shaawa, idan kinada kiba, zai dawo neman slim, idan slim kike zaidawo neman mai kiba, idan kina gajeruwa zaije neman doguwa..!!!



KIDAINA WAHALAR DA KANKI KO KASHE KUDIN KI KO LALATA LAFIYAR JIKIN KI WAJEN CANJA HALITTAR KI ZUWA YANDA NAMIJI KE SHA'AWA...

Abu na farko.... Duk yanda kike sai namiji ya nemi akasin haka a jikin wata. Misali idan kyakkyawa kike sai yaje neman mummuna, idan fara kike baka zata bashi shaawa, idan kinada kiba, zai dawo neman slim, idan slim kike zaidawo neman mai kiba, idan kina gajeruwa zaije neman doguwa da sauran su.. Haka Allah yayi namiji bawai son zuciya bane ko neman cin zarafin ki.

Abu na biyu... Mata suna neman kiba suna shan magunguna masu hatsarin gaske kamar shaka fashe (Dexamethasone ko prednisolone) da sauran su dan neman kiba, wai saboda ace suna cikin daula ko kuma mijin su yafison mai kiba.. Tambaya anan, yasan yafi son mai kiba ya aureki kina slim?

Abu na uku.. Kiba ta kasu kashi 3 akwai kibar (gado) daga uwa ko uba ko cikin dangi.. Wannan ko ya kikayi sai kinyita,  akwai kibar haihuwa, wata tana slim amma da ta haihu zatayi wannan kibar Naturally, akwai kibar hutu da cin abinci wadatacce.... Duka wadannan kibobin basuda illah, amma kin kasance bakida ko daya daga cikin wadannan dana lissafo kuma baki cikin kwanciyar hankali amma kice kiba kike so, duk kibar da kikayi sai ta zame miki illah,
Ku dube masu kibar magani (sha kafashe) zakuga wuyan su yayi kato huskar su ya kumburo, kirjin su yayi kamar drum 🛢 da katon ciki da siraran Kafafuwa kamar sauro🦟🦟🦟🦟. Mutum yayi babu kyau 😕😕😕sannan bazasu kara samun isassashiyar lafiya ba.

Ko yaya kikayi kokarin gamsar da namiji sai ya nemi wata, in kuma kikaga bai nemi kowa ba, tohh daman shi mai self discipline ne, ko yaya kike zaya zauna dake a hakan.... Ko family planning kikayi ya canja miki halitta ko kika daina haihuwa wata zai auro yasami haihuwa karshen tama ya sake ki....

Gyaran jiki yanada kyau kuma kada ki zauna Gajab kamar kayan wanki ba tsafta ba shafe shafe, amma kada ki canja tsarin jikin ki ko halittar ki da zaya iya haddasa miki wata rashin lafiya akan namiji kamar neman kiba ko bleaching ki zama fara....

A asibiti muna samun cases da yawa na rashin lafiyar mata akan shaye shayen magungunan kara kiba ko slimming da sauran su.... Wani infection dinda macce ke fama dashi sanadiyyar magungunan kara miima ne na gargajiya...... Azo ayita wahala.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAN MU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group din mu na Telegram Anan

👉 @MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/maasumahNews/

DOMIN BA DA SHAWARA KO AIKO DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post