MAGANAR SHEIKH ZAKZAKY (H) A RANAR 12/12/2015

 


Wallahi karyane! kasan dai yau shekaranmu 37 cur muna
harkar nan, sau nawa muka taba kai wa wani hari?. Soja yake
ko dan sanda ko wani mutum. Wai har munyi kokarin halaka
Tukur Burutai, Sau nawa soja na wucewa ta Husainiyya?
Yaushe aka taba kai wa wani hari?Ina ganin da ma kame kame
suke yi .

Yanzu haka an yi mana kawanya. Tun sama da awowi 12 suke
ta harbi a kan gidana. Sun rusa mana Husainiyya da manyan
bama -bamai, yanzu kuma suna kawo hari gidana. A yanzu
haka ma suna harbin bangwayen gidan ne. Sun zo nan tun
misalin karfe 10:00 na dare ranar Asabar. Kuma tun lokacin
harbi suke yi kawo lokacin da muke maganar nan.
Hakika rayuwata tana cikin hatsari. Amma ba abin da na iya yi,
Allah ne kawai zai kubutar da ni, saboda ba wata mafita. Sun
riga sun yi wa gidan kawanya. Suna kowa ne lungu da zai iya
kawo wa zuwa gidan nan. Ya zuwa yanzu da nake magana ba
mu san adadin mutum nawa suka kashe ba.

- Sheikh Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky (H) a ranar 12/12/2015,
Ranar da Gwamnatin Nijeriya ta afka masa a gidansa dake
Gyallesu Zaria.

- Ibrahim Almustapha Saminaka

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post