Mafarkin da Nayi Da Annabi (s) Ya Qara min Yaqini kan Da'awarsar Sayyid Zakzaky (h)_Cewar Mlm Ado Isah Guda Ningi




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


" ANAN GASKIYAR TAKE,  KA BI SHI  "


Cikin rubutun dana taba yi a baya na bayyana dalilin da yasa na amsa da'awar Sayyid Zakzaky (H) cikin shekara ta 1992 a makarantar koyon Ilimin kimiyyah (Government science secondary school) dake garin Azare ta Jihar Bauchi. 


Duk da cewa na manta cikakken mafarkin da kuma shekarar da nayi shi, amma na riqe maganar da Annabi (S. A. W. W) yayi min cewa :


" ANAN GASKIYAR TAKE, KA BI SHI. "


Cikin mafarkin nawa na ganni cikin wata tawaga mai yawa suna sauraron jawabin Sayyid Zakzaky (H),  sai wasu jama'a suka zo da muggan makamai (weapons) suka dira kan wannan jama'a har suka kai ga Sayyid (H) suka rufa a kansa har yakai qasa. 


Jama'a masu yawa daga cikin masu sauraron jawabin sun tarwatse, sai wasu daga cikinsu suka ce kowa ya kwakkwanta ya dauke numfashinsa (to lay down and take up their breathe), hakan zai taimaka wajen rage cutuwa daga abinda ake musu. 


Bayan mun kwankwanta mun dauke numfashin namu sai naji kamar zan mutu, sai na tashi ina gudu ! Kwatsam naci karo da wani mutum mai dararen kaya ya tsare ni yace :


" GUDUN ME KAKE YI? "


Nace, wa'azi muke saurare sai wasu suka zo da muggan makamai suka dirar mana har suka kai kan wanda muke sauraronsa. Bayan mun kwankwanta qasa mun dauke numfashinmu sai naji makar zan mutu, shine na tashi da gudu  !


Sai yace min : " NI MANZON ALLAH (S. A. W. W) NE, KA KOMA INDA KA TASO, ANAN GASKIYAR TAKE, KA BI SHI. "


Daga nan na dawo gurin dana tashi ba tare da jin tsoron mutuwar da tasa na tashi da gudu ba. Tun daga nan na qara samun yaqini kan da'awar Sayyid Zakzaky (H). 


Akan haka na cigaba da biyayya tare da qara sallamawa gare shi har zuwa waqi'ar Hussainiyya/Gyallesu wacce akayi a shekara ta 2015 wacce ta tuno min da wannan mafarki, sai dai Allah bai bani izninin wannan rubutu ba sai yau. 


YAA ALLAH KA TABBATAR DAMU QARQASHIN JAGORANCIN SAYYID ZAKZAKY (H)  


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


25th November, 2022/2nd Rabi'us-Sani, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post