Mace tagari Aljannar Duniya...!


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE

Dikkan yabo da godiya Suntabbata ga Allah Ubagijin talikai Ubangijin Al'arshi Mai girma. Tsira da Amincin Allah Su kara tabbata ga Mafificin halitta Shine Muhammadur-rasulillah (Saww).

= WACECE MACE TAGARI???

Ba muyi dubi da wannan Hadisi na Manzon Allah (saww) da yake cewa; ”Duniya gidan jin dadice Amma Mafi alkhairin abin jin dadin duniya itace Mace ta gari”.

1. Mace tagari, a Matakin farko tana kusantar Mijinta ne domin ta fahimci 'Dabi'u, Halaye, da Bukatun Mijinta domin ta san yadda zata zauna da abinta(Mijinta).

2. Mace tagari, Itace wacce tayi fice da kwarewa tare da d'aukaka Soyayyarta wajen Inganta bangarori Kamar haka:-

- Iya kwalliya
- Iya kallo
- Iya girki
-  Iya rakiya
- Iya tarba
- Iya Murmushi
- Iya magana
- Iya hira
- Iya tafiya
- Iya raha
- Iya rarrashi
- Iya konciya
- Iya kwantar da hankali da sauransu....

3. Mace tagari, Babban burinta Shine, Cika Siffofin da Manzon Allah (S) Ya siffanta mace tagari dasu.

4. Mace tagari, Tana zaman aure ne domin samun yardar Allah da lazimtar addu'o'i da kyautata ladubban tarbiyyya ta Addinin Muslunci a gidanta da 'Ya'yanta. Tana kiyaye Ibadu da kamanta tsoron Allah (t) a dukkan al'amuranta.

5. Mace tagari, Tana maida hankali akan kyakkyawar rayuwar ilimi acikin gidanta da yaranta domin samun albarka da hasken rayuwa.

6. Mace tagari, Itace Mai tausayawa Mijinta .

7. Mace tagari, Itace Mai tarbiyyantar da yaranta akan hanyar gaskiya ta yadda duk inda yaranta suka shiga zasu zama abin Sha'awa,abin so awurin Mutane.

8. Mace tagari, Itace Mai kishin mijinta, Kishin gaskiya bawai kishin hauka da wasu matan keyi ba.

9. Mace tagari, Itace Mai amfani da iliminta gun daya dace tayi amfani dashi.

10. Mace tagari, Itace Mai biyayya ga Mijinta, Mai kare dukiyar Mijinta a kowa ne irin yanayi da yake ciki.

11. Mace tagari, Ko kadan bata yadda tayi Munafincin mutum ko gulman mutum.

12. Mace ta gari, Takasance Mai shigar mutunci, Misali; Sanya Hijabin da zai rufe Mata ilahirin jikinta yayin fita Unguwa ko ga wanda ba Muharramanta ba. 

= GIDA NAGARI.

Gida ne da ake neman kusanci da Allah Matuka, Ta hanyar raya gidan da Nafiloli bayan an cika farillai. Ma'abotan wannan gida masu yin tsere da taimakakkeniya ne domin Neman yardar Allah acikin su, Suna masu yima junansu Nasiha ta gaskiya da Hakuri tare da tunkud'e Mummuna da kyakkyawa, Babu wani al'amari da zai fitine su ko ya kuntata musu face suna samun Mafitarsu ne ta hanyar Haquri da Sallah, Kamar yadda Allah yayi Qira ga Muminai a ayata 45, Acikin Suratul Bakara{“Haka kuma Idan wani al'amari ya dameshi to sai ya tashi yayi Sallah”.}Abu Dawud 4211.

= GIDAN MIJI.

Gidan Miji, Masarauta ce ga Mace, Shiyasa Mace tagari ita take iya Sarrafa dukkan abinda ta Mallaka na Ilimi, Hankali, Wayewa, da Kwarewar rayuwa, Domin ganin ta mayar da Masarautarta Aljannar duniya, Wajen Kwanciyar Hankali , More rayuwa, da Cikakkiyar nutsuwa ga Uban 'Ya'yanta.

YA Ke 'YAR'UWA MAI DARAJA, KISANI

- Gidan Mijinki, Shine filin jihadinki
- Gidan Mijinki, Shine Masallacin ki
- Gidan Mijinki, Shine Makarantarki wanda acikinta zaki kawatar da yara Manyan gobe
- Gidan Mijinki, Shine Mutuncin ki
- Gidan Mijinki, Shine rufin asirinki
- Gidan Mijinki, Shine Martaba da Daraja da Jin dadin ki
- Gidan Mijinki, Shine filin daaga, Anan gidan zaki nemi aljannarki,

'YAR'UWA

- Mijinki Shine Abokin Rayuwarki
- Mijinki Shine 
- Mijinki Shine Abokin Wasanki
- Mijinki Shine Abokin Shawarar ki
- Mijinki Shine Abokin Tattaunawar ki
- Mijinki Shine Maganin Matsalar ki
- Mijinki Shine Tiket dinki na shiga Aljanna Idan kin kyautata masa kinmar biyayya kunyi zama dan Allah babu cin amana.
- Mijinki Shine Tiket dinki na shiga wuta, Idan kika sa'ba masa ki kaqi yimar biyayya akan abinda bai Sabama Allah ba, to fishin Allah ya tabbata a kanki.  Allah Ya Tsaremu...

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post