Ma'aunin Gane Aboki na Gari

 


Zan so mai karatu yayi hakuri wajen karanta wannan rubutun nawa wata kila zai fahimci sakon danake so na isar

Menene kudi ? Wasu sunyi dogon sharhi sosai akan menene kudi. Har na tuno da wata karin magana da hausawa suke cewa ko mahaukaci yasan naira, Idan zamuyi la'akari cewa dukkan wata ftina ta duniya 75% anayintane saboda dukiya . Awannan lokacin kudi yana taka muhimmiyar rawa wajan tarwatsar da Alaka mai karfi wadda aka jima da gina ta.

 Zan so nayi tsokaci akan tasirin da kudi yakeyi a tsakanin abokanai.. Ma'aunin gane aboki na gari a wannan zamanin suna dayawa sosai amma Akwai hanya mafi sauki dazaka gane aboki na gari shine ka jarrabeshi da kudi

Dukkan wani abokin ka dazai cire kudinsa domin yashare maka hawaye a lokacin dakake tsananin bukatar hakan batare da kasani ba ko kuma dasaninka  wannan abokin ka rikeshi hannu biyu biyu

Zaka gane matsayinka a wajen abokinka a lokacin da ka karbi kudinsa bashi ko kuma wani kaya da yake sayarwa idan ka karba ba tare da kabashi kudinba  ta wannan hanya zaka gane yaya tsakanin ku yake da abokinka.

 Dukkan wani aboki da zai baka kayansa ko kuma cash money batare daya tambayeka ba. ko koma yabiya maka wata bukata a lokacin dakakeson hakan . Tabbass wannan abokin na gari ne 

Abin Alakari nasan wani zaice  ina nufin sai ta bangare kudi ake gane abokina na  gari ?  Tabbass dukkan nin wadda zai bayar da dukiyarsa akanka ba karamin masoyinka bane

Tabbass duk wani abokinka indai matsalar kudi bata hadaku ba bazaka taba gane yaya abotarku takeba

WANNA RA'AYINANE 

SAEED MUHAMMAD SALEH


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAN MU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group din mu na Telegram Anan


👉 @MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/maasumahNews/


DOMIN BA DA SHAWARA KO AIKO DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post