Kwadayi Mabudin Wahala

 


Bismillahir rahmanir rahim.

Takaicecen sakona zuwa ga yan uwa mata Almajirin sayyid zakzaky (h) (musamman yan mata) hausawa sunce duk wadda yahau motar kwadayi zai sauka a tashar walakan ci. Sisters sai dai kuyi hakuri yau. domin Alkalamina zaiyi sharhine akan halayar wasu sisters.

 Azahirin  gaskiya gwagwarmaya tazama sha kuru kundum. Kowane irin mutum Akwai. shin menene yake kawowa sister suke fadawa tarkon wasu brothes masu muna nan dabi'un????


Kwadayi da dogon buri


Kwadayi shine abu na farko dayake jefa wasu sisters cikin wani mugun yanayi a wannan lokacin.  saboda dayawa brother masu wannan dabi'ar suna ammfani ne da kwadayi da sisters din suke dashi wajen cimma burinsu . Zakaga sister kawai kun hadu a social media  amma tana tambayar ka kabata kudi koka tura Mata data ko kunya babu balle tsoron Allah. Tabbass in har baku canja haliba  to waddanna masu mugun halin bazasu fasa bata tarbiyar ku ba 


Abu na biyu shine dogon buri .sisters  yanzu basa duba waye yazo neman Auran su abinda sukafi dubawa sunfi son saurayi dan gaye mai daukar wanka wadda bashi da mata, sannan mai abun hannunsa. Wannna wata hanyace wace ake amfani da ita wajen cutar da sisters. Naji wata sister tana cewa wai laifin brothers din ne idan kaga sister kana sonta koda tana da  hali marar Kyau yakamata katsaya ka canja ta!! . Ga amsar dana bata. Yaushe ma tatsaya ta saurarenka balle ku fahimci juna balle tagane abinda takeyi babu kyau

 

GYARA KAYANKA 


Azahirin gaskiya yawancin mu duk addini ne yahadamu, Manzon Allah (s) ya kwadai tar damu wajen zabar miji na gari ko mata ta gari manzon Allah (s)  ya ummarcemu da Auran mace ta gari shine mafi Alkairi .haka kema sister dolene kizabarwa yayanki uba nagari. Yakamata mucire son zuciya muyi abinda yadace damu.

Muna rokon Allah ya tausaya mana 


Allah ya karawa su sayyid zakzaky (h) lfy da isan kwana



SAEED MUHAMMAD SALEH


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARAN MU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group din mu na Telegram Anan


👉 @MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/maasumahNews/


DOMIN BA DA SHAWARA KO AIKO DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post