KUJI WANNAN:- Ka ɗauka cewa matarka itace ƙawarka a cikin gida wacce za ta maye maka gurbin abokananka na waje




KU ABOKANAN JUNA NE.
-
❝Ka ɗauka cewa matarka itace ƙawarka a cikin gida wacce za ta maye maka gurbin abokananka na waje, kuyi wasa da dariya da ita. Ki ɗauka mijinki shi ne abokinki wanda zai maye miki gurbin ƙawayenki na waje, kuyi wasa da dariya dashi. Kada ku ɗauki junanku tamkar abokanan gabar da za su ke juyawa junansu baya. Ku taru ku farantawa junanku rai, ku mori rayuwar aurenku ta hanyar nuna salo na soyayya da kulawa, haƙiƙa za kuji daɗin junanku❞
-
"Kar ka taɓa ji a ranka cewa matarka tamkar wata baiwa take a gurinka wacce ba ta da wani kaso na haƙƙi a tattare dakai, haƙiƙa idan kayi wannan tunanin, to tabbas ka jahilci zamantakewar auratayya"
-
"Kar ki taɓa ji a ranki cewa mijinki ba wani bango bane na rayuwarki wanda za ki jingina a jikinsa biyan dukkanin buƙatunki waɗanda suka ɗamfaru a gareshi, kada ki maishe shi abokin faɗanki abin tozartarwarki, haƙiƙa idan kika yi haka kinyi butulci a gareshi"
-
Allah ta'ala ya zaunar da ma'auratanmu lafiya a gidajen aurensu, Ameen.
-

✍️ Journalist Ɗan Fudiyya




Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post