Umma Zeenat Ibrahim Zakzaky (H), Mata ce ga Jagoran Harka Islamiyya Sayyid Ibrahim Yaqoub Al-Zakzaky (H).
Ta kasance tare da Shehin Malamin tun a farkon fara Da'awarsa, don kusan zan iya cewa kowa a Harka Islamiyya, imma dai ya isko ta a matsayin Mata, kuma Uwar 'Ya'yan Sayyid (H) ko kuma yazo a lokacin da take cikin Manya Manyan Almajirai na farko farko (Kafin aurensu kenan).
Amma wannan rubutu ba zanyi shi bane domin nuna ta a matsayin Mata kuma Uwar 'Ya'yan Jagoran Harka Islamiyya(wannan ma karamin matsayi bane), a'a zanyi shi ne domin bayyana Wacece ita a Harkance, Gudummuwar da ta bayar, da kuma matsayin da take dashi a wurin Allah Ta'ala!
1. Malama Zeeanat ita ce Mace ta farko da ta fara sanya kammalallen Hijabi a kaf wannan kasa ta mu ta Nigeria. Na san ba zaku dauki hakan a matsayin abin jinjinawa ba ko? Amma kuyi wani nazari mana;
Nigeria kasa ce da take da tarihin kasancewar ta kasa ta musulmi, wadda har ma an taba Jaddada musuluncin a jikinta. Sannan kasa ce wadda take da Al'umma sama da milyan dari biyu, wanda mafi yawancinsu musulmi ne!
Ashe wannan ba abin jinjinawa bane, ga Macen da ta zama ta farko a dabbaka dokar Allah akan Hijabi, a irin wannan kasa ???
2. Na san dukkanmu Almajiran Sayyid (H) ne, wadanda kullum muke fada cewa "Bid dam, war ruh, labbaika Ya Al-Zakzaky"
Wato mun yadda zamu bada jininmu da rayukanmu domin kare Jagoran mu Sayyid Zakzaky (H).
Amma shin kowannen mu ne yake dabbaka hakan a aikace ?
Malama Zeenat tana cikin wadanda suka dabbaka wannan kalmar a aikace, bari in dan tunatar daku...
i. Itace wannan wadda ta sha duka da mari da dauri akan wannan Harka da Jagoranta.
ii. Itace wannan wadda tun kuruciyar ta ake fafutuka da ita a Harkar nan, har zuwa manyantan ta.
iii. Itace wannan wadda a lokacin da babu wani mataimaki (a mabiya) da ya rage ga Al-Zakzaky (H), ta tsaya kyam a gaban manya manyan bindigogi da sauran miyagun makamai, aka mata ruwan wuta kamar filin atisayen harbi!
iv. itace wannan wadda ta rasa lafiyar kafafunta duk a sanadiyyar wannan Harka Islamiyya da kuma kare Jagoran ta (H).
(Tare da cewa dukan mu mun sani, a lokacin da tayi wannan sadaukarwar, wasu da ake gani manya kuma abin koyi, ba a san wace duniya suka shige ba).
3. Kowa ya san girma da matsayin Shahidi a tafarkin Allah, domin ko ba komai Jagoran mu (H) ya sha fada mana. Uwa uba kuma ga Ayoyi da Hadisai rututu a kan girma da matsayin Shuhada.
Malam Zeenat Uwa ce ga irin wadannan mutanen (Shuhada) guda Shida, tayi renon cikinsu wata Tara, sannan ta haife su, ta kuma rene su akan Addini, wanda har suka girma suka samu matsayin da suka samu.
Lallai wannan ba karamin matsayi bane, bana jin a cikin Harka Islamiyya akwai wata Uwa wadda ta rasa 'Ya'yan cikin ta Shida, kuma Uku daga ciki an kashe su ne a gabanta, daga bisani itama akai mata barin wuta kamar a filin yaki.
Lallai wannan ba karamar Jarabawa bace!
4. Kamar yadda muka sani ne cewa, gwargwadon matsayinka a wurin Allah (T), gwargwadon Jarabawar da zai maka. Lallai an jarabci Malama Zeenat da Jarabawowi masu girma a rayuwa wanda babu wanda aka jarabta da irin su a Harkar nan, bayan Jagora (H).
Ashe hakan na nuna cewa babu mai irin matsayinta gun Allah (T) a cikin Harkar nan, bayan Jagora Sayyid Zakzaky (H).
Lallai idan har akwai Waliyyai a cikin Harkar nan (kamar yadda wasu ke nuna wa) ban da Jagora Sayyid Zakzaky (H), to babu Waliyyi ko Waliyyiya kamar Malama Zeenat Ibrahim Zakzaky (H). Domin zahiri Allah (T) ya bayyana mana girman sadaukarwar ta da matsayinta birbishin sadaukarwa ko matsayin duk wani mabiyi!
--Wannan kadan ne daga cikin girma da matsayin wannan baiwar Allah, a gurin Allah (T). Bayan kasancewar ta Mata kuma Uwar 'Ya'yan Mujaddadin wannan karnin; Sayyid Zakzaky (H).
A kullum burin kowane Dan Gwagwarmaya shine; Allah ya tabbatar dashi ya bashi Sabati irin na Malama Zeenat...
*(Wannan rubutu ne, domin tunatar da mu wace ce wannan Baiwar Allah da kuma matsayin ta a gurin Allah (T), a lokacin da wasu suke kokarin nuna ta a matsayin ba kowa bace ita bayan zamowarta Matar Jagora Sayyid Zakzaky (H)...*
5/4/1444H
31/10/2022M