Kishi ne ko Hassada?



@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 


Mafi akasarin mata Hassadace ke damunsu sai afake abayan kishi, Wato wannan kishin da wasu matan suke ganinshi amatsayin kishi to ba kishi bane, HASSADA ce,dan yana wuce qa'ida.  

1. MENENE KISHI ???!

  KISHI:-Ya kanzo da ma'anar "Gasa ko tsere da juna atsakanin matayen dake Zaune aqarqashin miji(1),

KISHI:- Halalne amusulunci,Matuqar Zaitaimakawa mace wajen neman yardar Allah,ta hanyar da gewa wajen yawaita ladabi da biyayya da kyautatawa mijinta,{MA'ANA} Kowacce mace takanyi Qoqarin ganin ta kula da Haqqoqin mijinta fiye da sauran abokan zamanta,dakyautatawa,da tarairaya,a shi damakusantansa danginsa,da yaransa dasauransu. 

Har kullum Zuciyar Dan Adam tana son mai sonta da kyautatamata,tana kuma qin mai qinta da munana mata,kyautatawa Sirrine na qara danqon Qauna tsananin ma'aurata,To wannan shine Halattaccen kishi wanda Addininmu ya yarjar mana da ita.
- IRE - IREN KISHI

KISHI,Sun kasu kashi - kashi,ba lalle sai kishin tsakanin matayen miji guda ba.(MISALI)

1, Akwai KISHIN iyaye,
2,Akwai KISHIN Dabi'u,
3,Akwai KISHIN Qasa,
4, Akwai KISHIN Karatu,
5, Akwai KISHIN So,
6, Akwai KISHIN Al'adu,
7, Akwai KISHIN Kai, 
Amma Almuhim Shine KISHIN  Addini,Wanda zamuyi bayaninsu nangaba insha Allah . 

Mafi yawan maza za' a Samu kowa yana da dalilinsa na qarin Aure,wasu dan rashin jin dadin xama da matar ne,wasu kuma kawai suna sha'awar zama da mata 2-3-4,ne wasu dan Qazantar matar ko rashin iya girki,soyayya,da magana da dai sauransu,

To sai ke ki duba shin mijinki awane dalili ne zai qara auren,idan har daga jikin kine wato laifin kine to saikiyi gaggawar gyarawa dan koda yayi auren zaki samu sassauci azuciyarki agunshi da kuma abokiyar zamanki. In ko Kinsan ba daga jikin kibane kawai yana sha'awar hakanne to sai ki rarrashi zuciyar ki,kada ki hana abinda Allah ya halatta,ki barwa Allah lamarinki,ki roqi mafi Alkhairi da daurewar zaman lapiya atsakaninki da mijinku da kuma abokiyar zamanki,Wannan Shine.

Sannan idan kishiyarki Abokiyar zamanki ta fiki iya wani abu wanda mijinki yake jin dadinsa,yake Kuma birgeshi,to ba hauka ko Baqin ciki zaki riqa yimatana,A'a ki daure kiga kinyi koyi da ita harma ki wuceta,dan kema kiriqa birge maigidanku,ba fada ba tashin hankali,ko daurin dankwali tayi ke baki iyaba megidanku kuma yana son irinshi,to kije ta koyamiki ba wani abu bane.

Dan haka ma'anar kishi Anan shine tsrere da juna,inko aka samu akasin haka to ba kishi bane Hassadace . 

Ina Qira da babbar murya ga Sauran mata da cewa ; Matuqar muna son rabauta aduniya da lahira,to muji tsoron Allah,mu kiyayi shirka dik qanqancinsa,mu kiyaye zurfafa kishi(wato Baqin kishi),Wanda ke makantar da ido da zuciya,ya raba mutum da imaninsa. 

___SHAWARA

Da zaran munji Alamar Hassada ya fara shiga zuciyar mu game da abokiyar zamanmu ko makusantanmu dan gane da wata ni'ima/falala da Allah yayi masa,to muyi hanzarin neman tsari daga Shaidan(LA),mu kuma yi Addu'ar Alkhairi awannan mutumin,Matuqar munyi haka,to nantake hassadar zai kau azuciyarka da yardar Allah. 

2. MENENE HASSADA???!
.. 

ATAQAICE:- Hassada Shine Mutum ya rinqa nuna baqin ciki Azuciya da kuma fili,dan gane da wata Rahma ko falala da Allah yake badasu ga bayinsa maza da mata.  

- ALAMOMIN MAI HASSADA KODA AKAN KANKA NE. 

1- Idan Allah ya azirta bawansa da ilimi,ilimin Al-qur'ani,ilimin Hadisai,ilimin fiqhu,ko ilimin kimiyya da fasaha,Sai mai hassada ya rinqa bakin ciki game da wannan ilimin da Allah ya bashi,to tamkar yana tuhumar Allah ne,dan me kabawa wane ilimi,ko yace Allah ka kwace wannan ilimin gareshi. 

2 - Idan kuma Allah ya azirta bawansa da mace tagari,kyakkyawa,ko 'yar manyan mutane,Sai kaji wannan me hassadar yana Cewa: Wane asararren ne ya aurer da 'yarsa ga wannan mutumin gata kyakkyawa gsky ancuceta da aka auramatashi,to tamkar yana tuhumar Allah cewa;Allah dan me ka Aurawa wannan mutumin wannan matar. 

Aqarshe,ya rinqa musu mummunar Addu'a,da cewa: Allah ya jefa fitina atsakanin su,ya kuma rabasu d gaggawa.  

Saide kuma su mata,sun fiye nuna kishinsu akan mata 'yan'uwansu,MISALI; Duk matar da Allah ya taimaketa ta auri,mutumin kirki ko mai,kudi ko mai mulki,idan har sun fiskanci zata huta,tofah zata fiskanci masifofi matsananci daga 'Yan'uwanta mata masu hassada,dan Kowacce tana burin dama itace amatsayin ta,sai suriqa fatan Aurenta ya mutu,su aure miji. 

To irin wadannan mata miyagune,suke zuwa wurin bokaye da matsafa,in basu samu,nasaraba sai su canza hanya suyita Qulle - Qulle,Dan karta haifu.  ASTAGFIRULLAH. 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post