TA YAYA ZAKI BURGE MIJINKI |
❝Idan kina son ki burge mijinki, to ki yawaita yin fara'a a gareshi, ki yawaita caɓa ado da kwalliya a gareshi, ki yawaita yin shagwaɓa a gareshi, ki yawaita furta kalaman soyayya a gareshi, ki dinga yin biyayya a gareshi a cikin dukkanin abin da bai saɓawa dokar ubangiji ba, idan kika lazimci hakan, tabbas mijinki zai so ki kuma zai ji babu kamarki a cikin ransa koda yaushe❞
-
"Kada ki zamto dunkunkuma wacce bata san yadda za ta burge mai gidanta ba, akwai hanyoyi masu yawan gaske da za ki bi domin kankaro girma da mutuncinki a gurin mijinki"
-
"Kada ki yarda girman kai ya hauki yasa ki kasa bin hanyar da mai gidanki zai ji cewa haƙiƙa yayi dacen samun macen da bazai taɓa yin nadamar kasancewa da ita ba"
-
"Ki nuna masa ƙauna ta dukkanin salon da kike iyawa matuƙar bai kaucewa hanyar Allah ba, haƙiƙa mijinki zai ƙaunace ki sosai"
-
Allah ta'ala yasa mu dace baki ɗaya.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com