da yawan mutum kai aikata wani abu wanda a zatonsa ba laifi bane, amma a shari'a girman laifin ya fi na wanda ke aikatawa.
Abinda ya kamata mutum ya lura dashi shine, tabbas duk wani mai aikata mummunan aiki kuma yaga ana tarayya dashi ba tare da an qyamace shi ba zai cigaba da aikata wannan aiki ne bisa ganin ana tare tare dashi, amma idan ya zamana yana aikatawa kuma qyamatar wannan aiki nasa ko ana hana shi, to, zai yi qoqarin bari ko rage wannan aiki nasa.
Ya zo cikin riwaya inda Imam Ali (A. S) ke cewa :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" الرَّاضِي بِفِعْلِ قَوْمٍ كَالدَّاخِلِ فِيهِ مَعَهُمْ وَلِكُلِّ دَاخِلٍ فِي بَاطِلٍ إِثْمَانِ إِثْمُ الرِّضَا بِهِ وَإِثْمُ الْعَمَلِ بِهِ.
" SHI YARDA DA AIKIN MUTANE (na muni) KAMAR WANDA KE SHIGA CIKINSU NE (yana aikatawa) TARE DA SU. GA DUKKAN MAI SHIGA CIKIN (aikin) QARYA YANA DA LAIFI BIYU (2).
LAIFIN YARDA DA SHI DA KUMA LAIFIN AIKI DA SHI. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Saboda haka a kiyayi yarda da duk wani aiki wanda aka san na qarya ne ko na muni, hakan zai taimaka wajen hana masu aikatawa. Amma muddin masu aikata mummunan aiki suna ji/gani ana qyale su haqiqa za su cigaba da aikatawa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
12th November, 2022/ 18th Rabi'us-Sani, 1444.