Jan Hankali:- JASAZ Ba Ta Da Shafuka A Social Media! _Muhammad Kaseem (Gwarzo




Muna amfani da wannan damar domin mu kara janyo hankalin yan uwa da al'umma baki daya, kan cewa; JASAZ ba ta da wasu shafuka a social media.


Fa'eez Media da ya ke kan Facebook zuwa yanzun, shi ne kadai shafin da za a samu abubuwa masu alaka da JASAZ.  


Wannan jan hankalin ya zamo dole duba da yanda wasu suka dage da sai sun buda accounts masu alamta JASAZ. Duk da ankarar da su da aka yi illar yin hakan, wasunsu ba su daina ba, wannan ya sa muke kyautata zaton hannun makiya domin bata muna suna ko aibata mu a idon jama'a. 


Saboda haka, muna kara jaddada ma al'umma cewa, duk wani abu da aka gani daga wasu shafuka masu alamta JASAZ wanda ba Fa'eez ba, lallai ba mu da alaka da shi, kuma aikin makiya ne. Allah Ya datar da mu. 


Sa Hannu: Muhammad Kaseem (Gwarzo) a madadin management.

24/11/2022


1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Kenan Duk Wani shafi fB ko makamantansu karmuyi laakari dasu

    ReplyDelete
Previous Post Next Post