ITA DUNIYA TAMKAR MACIJIYA CE !

 




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


KA NISANCI ABUBUWAN DAKE BA KA SHA'AWA DAGA CIKINTA 


Ita duniya gida ce wacce komai rashin dadinta ba a son barinta, kuma dadinta ya kasance mai rudar da mutane ko shagaltar dasu wajen barin tuna lahira gidan da ya zama na dawwama da alkhairi ga wanda ya kyautata a duniya.


Tana da kyau ko dadi kamar yadda shafar jikin maciji yake, sai dai sharrinta yayi kama dana macici tunda tana iya halakar da wanda yayi imani da ita. 




Ya zo daga Imam Ali (A. S) inda yake cewa :



قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):


  " إِنَّ الدُّنْيَا كَالْحَيَّةِ لَيِّنٌ مَسُّهَا قَاتِلٌ سَمُّهَا فَأَعْرِضْ عَمَّا يُعْجِبُكَ فِيهَا لِقِلَّةِ مَا يَصْحَبُكَ مِنْهَا وَكُنْ آنَسَ مَا تَكُونُ بِهَا أَحْذَرَ مَا تَكُونُ مِنْهَا ."


" ITA DUNIYA TAMKAR MACIJI TAKE, SHAFARTA NA DA DADI/LAUSHI, DAFINTA (poison) KUMA YANA KISA. (Saboda haka) KA KAWAR DA KANKA DAGA (dukkan) ABUBUWAN DAKE BA KA SHA'AWA A CIKINTA SABODA QARANCIN LOKACIN ZAMANKA (da za kayi) CIKINTA, KUMA KA KASANCE MAI GARGADI GAME DA ABINDA ZAI KASANCE DA ITA, KA TSORACI ABINDA KE KASANCEWA DAGA GARE TA (na rudi). "


المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم


A wani guri kuma yake cewa :


  " الدُّنْيَا سَمٌّ آكِلُهُ مَنْ لَا يَعْرِفُهُ ."


" ITA DUNIYA GUBA (poison) CE, MACIYINTA SHINE WANDA BAI SANTA BA. "



المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم


Ma'ana wanda yasan wacece duniya haqiqa ba zai damu da cin dadinta ba.


Wannan ita ce duniya, idan qyalqyalinta ya rudar da kai sai ta kaika ga halaka. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


22nd November, 2022/ 28th Rabi'us-Sani, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post