Iran Ta Shirya Sasanta Rikicin Dake Tsakanin Siriya Da Turkiyya

 


Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Hossein Amir Abdullahian ya bayyana cewa, Iran ta fuskanci damuwar da kasar Turkiyya take da ita dangane da matsalolin tsaron a iyakar ta da kasar Siriya kuma ministan Iran a shirye take tayi amfani da damrmakin da take da su domin taimakawa Turkiyyan ta kawo karshen matsalar.

A wata tattaunawa da Hossein Amir Abdullahian yayi da takwaran sa na Turkiyya Mevlut Cavusoglu a ranar talata 29 ga watan Nuwamban 2022, ya kuma bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take tayi amfani da hanyoyin diflomasiyya gami da siyasa domin sasanta gwamnatocin Ankara da Damascous.


A bangaren sa ministan harkokin wajen Turkiyya Cavusoglu ya kokawa Hossein Abdullahian barazanar tsaron da kasar sa ke fuskanta kuma ya bukaci irin wannan tattaunawar ta cigaba da gudana a tsakanin kasashen biyu makotan juna.







Sai dai a halin d ake ciki Turkiyya ta sanar da yiwuwar kaddamar da hare hare ta kasa a arewacin Siriya da kuma Iraqi.

”Nisan zangon da wannan hare hare zai ci ya danganta da abinda gwamnatin Turkiyya ta yanke hukunci, kuma anaiya fara kaddamar da hare hare gobe, sati mai zuwako kuma wata mai zuwa, sojojin turkiyya da kuma jami’an leken asirin ta sun lura da lamurran” kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Turkiyya Ibrahim Kalin ya sanar a ranar talata 29 ga watan Nuwamba 2022.

Shugaban kasar Turkiyya yayi da’awar kasar sa tana kokarin kai harin da sojojin kasa ne domin tarwatsa wani gungun sansanin kurdawa wadanda ke barazana da tsaron Turkiyyan.

Amma sai dai a daya bangaren Shugaban kasar Siriya Bashar Al-assad ya bayyana cewa kasar sa zata mai da martani yadda ya kamata ga duk wani hari da Turkiyyar zatayi gigin kaiwa.

Iran da Rasha sun wadanda sune manyan wadandake taimakon Turkiyya domin yaki da ‘yan ta’adda sun gargadi Turkiyya bisa wannnan kuduri na ta na kai hari Siriyan.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post