Imam Sadiq (A.s) Yana Cewa; 'Yan Shi'arsa: "Babu Wasu Mutane Biyu Da Zasu Ƙaurace Wa Junansu Face Guda Daga Cikinsu Ya Cancanci Barranta Da La'ana, Mai Yuyuwa Ma Dukkansu Biyun..."

 



SAKON BARKA DA JUMA'A: ƘAURACEWA JUNA!


____Hassan Abubakar Ɗan Sister Katsina.

Imam Sadiq (A.s) Yana Cewa; 'Yan Shi'arsa: "Babu Wasu Mutane Biyu Da Zasu Ƙaurace Wa Junansu Face Guda Daga Cikinsu Ya Cancanci Barranta Da La'ana, Mai Yuyuwa Ma Dukkansu Biyun..."

Sai Wani Daga Cikin Sahabbansa Ma'atab Ya Tambayeshi Cewa; "Allah Ya Sanya Ni Fansa Gareka, Hakan Ga Wanda Yayi Zalunci Kenan To Shi Kuma Wanda Aka Zalunta Minene Laifinsa?"

Sai Imam (A.s)  Ya Amsa Masa Da Cewa; Saboda Bai Kira Dan'uwansa Zuwa Ga Sulhu Ba, Sannan Kuma Bai Kau Da  Ido Daga Kalaminsa Ba. Haqiqa Naji Babana Imam Muhammad Al'Baqir, Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gareshi Yana Cewa; Idan Mutane Biyu Sukayi Faɗa: Sai Guda Ya Zagi Dan'uwansa, To Wanda Aka Zalunta Ya Koma Zuwa Ga Abokin Nasa Yace Masa:

Ya Dan'uwana Ni Ne Mai Laifi Don Ya Toshe Giɓin Da Ya Shiga Tsakaninsa Da Abokin Nasa. Saboda Allah Ya Maɗaukakin Sarki Mai Hukunci Da Adalci Ne Yana Karɓar Haƙƙin Wanda Aka Zalunta Daga Wanda Yayi Zalunci.

H. Ɗan Sister Kt
07069526713

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post