-Imam Sadik (AS) Yace: "Haƙiƙa a Cikin Aljannah Akwai Wani Matsayi da ba Wanda Zai Kai Gare shi, Sai Bawan da Allah Ya Jarrabe shi da Wata Musiba a Jikinsa"

 


-ALLAH KA TAUSAYA MANA.


-Manzon Allah (S) Yana Cewa: "Haƙiƙa Allah Ta'ala Yana Shayar da Muminai Bala'o'i Kamar Yadda Uwa Take Shayar da Jaririnta Nono." 


-Imam Sadik (AS) Yace: "Haƙiƙa a Cikin Aljannah Akwai Wani Matsayi da ba Wanda Zai Kai Gare shi, Sai Bawan da Allah Ya Jarrabe shi da Wata Musiba a Jikinsa"


-Imam Sadik (AS) Yace: "Haƙiƙa Allah Ya kan Ajiyewa Bawansa Wani Matsayi A Aljanna, Amma Ba Zai Kai ga Matsayin Ba Sai An Jarraba shi da Ɗayan Abubuwa Biyu:


(1) Ko A Jarrabe shi da Tafiyar Dukiyarsa, 


(2) Ko Kuma A Jarrabe shi da Wata Musiba A Cikin Jikinsa"


-Manzon Allah (S) Yace: "Ina Mamakin Muminin da Yake Yin Raki Akan Rashin Lafiya da ta Same shi, Alhali da Ya san irin Abin da Yake Cikin Rashin Lafiyar Na Alkhairori da Yayi Burin Kada Ya Warke Har Lokacin da Zai Haɗu da Ubangijinsa Mai Girma da Daukaka"


-Imam Ali (AS) Yace: "Idan Ka ga Ubangijinka Yana ta Saukar Maka da Bala'o'i, to Ka Gode Masa, idan Kuwa ka ga Yana ta Kwararo Maka Ni'imominsa to Ka ji Tsoronsa".


-Shi Kuma Imam Bakir (AS) Cewa Yayi: "Ni Ban Damu ba in Wayi Gari Ina Matalauci, Ko Mara Lafiya Ko Mawadaci, Domin Kuwa Allah (SWT) Yana Cewa: Ban Aikata Wani abu ga Mumini ba Face Abin da Ya fi Zame Masa Alkhairi".


-Kuma A Wani Hadisin Yana Cewa: "Haƙiƙa Ana Jarraba Mumini Anan Duniya Dai-Dai Ƙarfin Addininsa".


-A Wani Hadisin Kuwa Cewa Yayi: " Duk Lokacin da Bawa Ya Ƙara Samun Imani, Za'a Ƙara Takura Masa Al'amarin Rayuwarsa".


-Imam Sadik (AS) Yace: "Mumini Ba Zai yi Kwana 40 Ba Face Allah Ya Bijiro Masa da Abin da Zai Saka Masa Baƙin Ciki "


-Imam Sadik (AS) Yace: "Idan Allah Ya So Bawansa Sai Yayi ta Zubo Masa Bala'i, Ba Zai Fita Daga Wani Baƙin Ciki ba Face Ya Sake Faɗawa A Cikin Wani Baƙin Cikin."


-Daga Littafin Biharul Anwar. 


-Allahu Akhbar! Sayyida Zainab (AS) Lokacin da Aka yi Musu Gayar Cin Mutunci da Wulaƙanci A Karbala, Sai Yazidu Ya Kalle ta Yana Dariya Yace: Kin ga Yadda Allah Yayi Daku Ko? Sai Tace Masa: "WALLAHI NI KAM BAN GA KOMAI BA FACE ALKHAIRI".


-Ya Allah! Muna Godiya Agare ka da Kake ta Jarraba Mu Da Fir'aunonin Wannan Ƙasar, Lallai Mun San Wannan Tagomashi Ne da Girmamawa Agare mu Daga Wajen ka,


-Ya Allah Ka Bamu Dakewa da Sabati A Bayan Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) Komai Tsananin Bala'i da Musifa.


-Muhammad Jiddah Nguru.

07037009525


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post