SAYYID IBRAHIM YAQIN EL_ZAKZAKY (H) |
Imam Ali (as) yana cewa "ranan taskun azzalumai yafi zafi fiye da zafin zaluncin Wanda aka zalunta a gidan duniya"
Buhari ya tafka zalunci 2. Rashin cika alkawari wa wadanda suka zabe ka, sai kashe wadanda suke kira Zuwa ga tabbatar da addinin Musulunci, cikin su har da wadanda suka zabe k
Duk yan Nigeria da wadanda suka zabe ka da yan adawa da wadanda ma basu yi zabe ba, kamar ni da wassu kenan, kundin sarin mulki ya ce ka tsare rayukan su da dukiyoyin su ba tare da nuna bambanci ba
Da farkon farawa ka diram ma yan Shia'a, ka so ka Murkushe su, kwata kwata! Amma Allah bai nufa ba, Allah ya so addinin Sa ya tabbata mulkin zalunci ya gushe. Kayi tasyuwar daga don Murkushe Sheikh El-zakzaki H da almajiran sa amma Allah mai karfin da babu I tasa ya nuna maka ba ka isa ba. Kashe rai bada hakki ba sakamakon sa, dawwama a cikin jahannama. Wanda Allah ta'ala ya fadi hukuncin Sa a Al qur'ani . Ka zalunce mu, ba mu yafe ba, ba mu manta ba, zalunci ma fi muni Wanda sakamako yana jiran ka, za ka fara gani tun daga nan duniya sannan gobe kiyama
Sai zalunci na biyu, rashin cika alkawari, da rashin tsaro na rayuka da dukiyan yan Nigeria kamar yadda kundin mulki ya tanadar, amma ka yi fatali da shi, kulli yaumin sai an kashe, sai an sace, tare da amsan kudin fansa. Maganan ruwa da wutan lantarki, da asibiti, da hanyan mota dss ba ka ma San su ba. Wannan ma abin tambaya ne gobe kiyama, Allah ya yi umurni da cika alkawari kuma rashin cikawa abin tuhuma ne gobe kiyama
Mr Buhari! Ka dai ji yadda Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaki H yace da ku masu neman ganin bayan sa, cewa za ku tsaya a gaban Allah gobe kiyama don amsa laifin ku da sakamakon ayyukan ku. Amma sai naga tamkar kara maka fandara ne saboda ban ji ka nemi yafiyar su ba. Amma na fahimci, baka tsoron Allah ballantana ukubar Sa. Duk mai digon imani a zuci, ba zai aikata wannan dayyen aiki ba, ballantana ma ace masa Allah ya isa ya yi biris. Mulki zai kare! Ina mamakin mai musun mutuwa alhali gashi ana mutuwa a gaban sa. Mutuwar ka akwai kallo haka lahilar ka, abin kallo ne. Allah ya isa! Buhari Allah ya isa! ! Buhari Allah ya isa!! Allah ya sa kayi mummunan karshe da zai zama wa'azi ga azzaluman baya. Sheikh El-zakzaki H Allah ya saka muku, ya kara muku hakuri da lafiya, ya cika muku burin ku na tsamar da wannan alumma daga duhun jahilci da kaskancin duniya da lahira Zuwa ga daukakan duniya da lahira.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com