Illar dake Cikin kin Saka Hijabi ga 'Ya Mace!!!



@MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE 


Ta ki bin umarnin Allah(ta'ala), ta ki yimasa biyayya, tabar wajibi daga cikin wajibai wanda Allah ya wajabta mata, to tamkar tabar Salla da Azumi ne, Tinda duk cikarsu wajibai ne akanta. Sakamakon sabawa Mahaliccinta da tayi, da zata mutu a wannan rana Wuta zata.

Barin hijabi zai haifar mata da matsaloli na rayuwa, Kamar Zuban mutuncinta, Zata zama bata da Daraja da kima, da Soyayya a idon Al'umma. Zata rasa kamalarta. Domin Daraja da Mutunci, da 'Daukaka da kima da kamala, da kuma soyayyar Mutane, Dik suna samuwa ga mace mai saka kammalallen Hijabi.   

Amma abin takaici, Zaka ga mace ta caba ado tana tsiraici a kan titi, Idan kayi mata Nasiha Sai tace, "Imani yana a zuci ne, ba a fuska ba"  Hmm! "Labarin zuciya a tambayi fuska".  Allah Yasa Mudace. 

                              

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post