ya zaman dole ga musulmi se yayi bara'a sannan y mika wulaya, wadannan abubuwa guda biyu tare suke tafiya, dan haka a cikin Qur'ani me girma Bara'a ce ta fara zuwa sannan wulaya, idan aka samar d wulaya babu bara'a ba ze zama me amfani ba, haka ma idan akayi bara'a babu wulaya shima babu wata natija, matakin farko shine ka kadaita Allah(swt), kafin mutum y kadaita Allah se ya cire komi d kowa a zuciyarsa, se y gamsar d kansa Allah kadaitaccene daga abokin tarayya, yayi bara'a ga komi, sannan ya kadaita Allah, yayi wulaya kenan,
Mataki na biyu: wulaya ga manzo(saw), akwai manzanni d suka zo kafinshi, daga ji6intar Al'amari ga Annabi(s) dole kayi imani da manzanni d suka zo kafinshi sannan ka tabbatar da nashi, amma kuma shine mafificinsu (saw),
Mataki na uku: yin imani da wasiccin Imam Aliyu(as) da manzon Allah(saw) yayi a bayan wafatinsa, bayan wafatin Annabi(s) dole ne mutum yayi imani da cewa babu wani da za'a ji6inci Al'amari gareshi se imam Ali(as) da sauran khalifofi da suka biyo bayansa na karshen su Sahibul Asar(ajf),
A wannan zamani da imam Mahadi(ajf) ke cikin gaiba, shine lokacin da yafi kowanne hadari ga Al'umma, domin da yawa zasu kuskure wurin gwama matsayinsa da wasu, wanda aikata hakan na iya gur6ata aikin mutum kacokaf, dole ne se anhada da taka tsantsan da kiyayewa,
DAGA TAFSEER & JAWABAN JAGORA
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com