Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Hijabi Ba kyallene kawaiba, hijabi Rigan kiyaye mutumci ne sai idan da mutumci dama a zuciya da gaba to sannan kyalle yake kyau , ko ba'a luraba ? Yanzun ana sanya hijabin zubargada, kamar ansamu cigaba dangane da hijab, a wannan nahiyar da ba'a san hijabiba mace kawai idan zata fita sai tai lullube , sai dai lullubi da gyalenta, ta yafa gyalenta sai ta fita , To in ta dawo sai ta cire gyalen ta yar,
To, agane shi hijabi anayima mutumne, ba anayi ma garine ba, anayiwa mutum hijab, saboda haka idan mace tana a cikin dakinta babu yuwuwar wani ya shigo dakin, inba yiwuwar wani ya shigo , akwai al'ada iri biyu 2 , kafin su shigo sai sun yaye labule in sukaji ba a kulle ba sai su cimimiye, sui ciki , inkuma sunji an kulle suce: A'ah ta kulle dakintane ? su murda sunason su shiga sui ciki abinsu ,
To idan ta aminta ba wanda zai shigo mata, to lokacin shikenan sai ta saki jikinta, amma in akwai yuwuwar wani zai shigo mata to dole ya zama tana da hijabi , kaga mutum ake ma Hijabi kenan , mutum dinnan kuma wanda yake ba muharraminta bane ,
shehin malamin ya sake mai maita cewa : mutum ake wa hijabi ba'ana ma gari bane, da yawan mutane an danka anayima garine hijabi , sabo da haka intana gidanta , gidan fa gashi katon gidane , da 'Dakuna daban-daban kilama irin wanda akece ma UNITED NATION din nan ne , kowa da matarsa , Hmmm (murmushi) wannan da matarsa wannan da matarsa , sai sufito tsakar gida su saki jikinsu , sui nasu harkoki , kowa yana shigowa , shikenan hijabi sai in zasu fita su danko su sa, amma in suna gida shikenan , kuma kowa yana shiga gidan ya gansu, to anyi mene kenan ?! mutum ake ma hijabi ba wajen gari ake ma hijabi ba, mutum ake mawa,
in mutum ya ya ganta a gida ba hijabi anyi mene kenan ?!, ko kazalika ainihin wasu sun dauka kawai anayima gari ne ba mutum, mutum akema hijabi a fahimci wannan saboda haka ko da a dakin tane indai za'a gantaba hijabi to tasa hijabi , yawwa! ba gari ake mawaba.
Shehin malamin ya bayyana hakan ne yayin tafseerin ayar Hijab, cikin suratul AHAZAB AYA TA 53, Wanda ni ibraheem Sani Fudiyyah Yankara na rubuto maku, Daga Audio din jawabin
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com
Masha Allah
ReplyDelete