WAFATIN SAYYADA FADIMA AL'ZAHARA'U YAR MUHAMMADU RASULULLAHI SAW.
Hakika zuciya ta tayi xafi idanu sunyi raurau badan komai ba saidan tuna abinda ya faru, a xamani magabaci Bayan wafatin manzon allah saw.
Domin Abubuwan da suka faru bayan wafatin Annabi (saw,)
da suka hada da cutar da al-Zahra (a.s.) sunkara zafafa mata ciwo da takaici, ta yadda har sai da suka bar ta a kwance cikin jinya.
Da matsanancin rashin lafiya har tsawon kwanaki arba'in. Duk da haka, a karshen rayuwarta ta nuna
alamun kamar ta warke, domin ta tashi ta sa 'ya'yanta Hasan da Husaini (a.s.) suka yi wanka,
ta sa musu tufafinsu, sannan ta bukace su da suje su ziyarci kabarin Kakansu Manzo Allah (SAW).
Duk da wannan alama na samun sauki, ashe ita shiri take yi na haduwa da mahaifinta; sai tabukaci Asma'u bint Umais da ta debo mata ruwan wanka, sai ta yi wanka ta sa mafi kyawun tufafinta.
Yayin da ta ji kusantowar ajali sai ta bukaci Asma'u da ta yi mata shimfida a tsakar daki, sai
ta kwanta tana mai fuskantar alkibla. Sannan sai ta sa Asma'u da Ummu Aiman da su kira mata
Imam Ali (a.s.). Da ya zo sai ta ce masa: "Ya kai dan baffa!, ina jin cewa kuma ni na zo karshe. Ba na jin wani abu face cewa ni zan
hadu da babana a 'yan sa'o'in nan. Ina so in yi maka wasici da abin da ke cikin zuciyata". Sai Imam ya ce mata: "Yi wasici gare ni da abin da kike bukata 'yar Manzon Allah", sai ya zauna daidai kanta, ya hori wadanda ke cikin dakin da su fita. Sai ita kuma ta ce masa:
"Ya dan baffa, ba ka taba samu na da karya ko cin amana ba, kuma ban taba saba maka ba tun da ka zauna da ni".
Sai Imam (a.s.) ya ce: "Allah Ya sauwaka, ai kuma kin sani, kin fi biyayya, kin fi takawa, kin fi karimci kuma kin fi tsoron Allah a kan in zargeki da saba min.
Hakika rabuwa da ke da rashinki sun tsananta gare ni. Sai dai haka wani abu ne da ba makawa kansa. Wallahi kuma kin sabunta min musifar rabuwa da Manzon Allah (saw), kuma hakika wafatin ki da rashin ki sun Girmama
Inna Lillah Wa Inna Ilaihi Raji'un!
Wannan musifa me ya fi ta daga hankali da zafafa rai da bakin ciki!! Wallahi musifa ce da bata da makoki, kuma bakin ciki ne da ba shi da masauyi.". Sai duk suka yi ta kuka na wani lokaci, sannan
sai Imam Ali (a.s.) ya kama kanta ya ka kirjinsa ya rungume ta ya ce: "Fadi wasiyyar da kike so, lallai za ki same ni mai cika ta, zan aiwatar da duk abin da ki ka hore ni da shi".
Sai Fatima (a.s.) ta ce:"Allah Ya saka maka da alheri, Ya kai dan baffa!, da farko ina maka wasici da ka auri 'yar 'yar'uwata Umamah , a baya na, domin ita zata kasance ga 'ya'yana kamar ni; domin mata dole ne ga maza.".
Har ila yau ta ci gaba da ce masa, "Ina yi maka wasici da kar (ka bar) daya daga Cikin wadannan da suka zalunce ni ya halarci jana'izata, kar ka bar waninsu ya yi salla a gare ni. Ka binne ni da daddare, lokacin da idanuwa suka natsu kuma gannai suka yi barci .Sai ta cika wasiyyarta
Fatimatul-Zahra (a.s.) ta yi sallama da Ali (a.s.) da 'yan gidanta, aka dauke ruhinta mai tsarki zuwa gidan dawwama da ni'ima. Sai mai shela ya yi shelar cewa Fatima ta bar duniya sai Madina ta dauki zafi, zukatan muminai suka buga saboda rasa bangaren Manzon Allah da reshen Annabci. Jin wannan labari, sai matan Banu Hashim, na Muhajirai da Ansar suka taru, mutanen Madina suka yi dandazo a kofar gidan Ali; masu hudubobi suka shiga tunatar da ranar rasuwar Manzo (saw) a gidan Fatima da kalmomi bakin ciki.
Taron jama'a na jira su ga an fito da al-Zahra (a.s) zuwa makabarta; sai dai Imam Ali (a.s.) ya umarci Salman - ko kuma Abu Zarri, bisa sabanin ruwaya - da ya sallami mutane, ya ci musu Fatima ta hana mutane su shaida jana'izarta kuma kar kowa ya shiga wajen gawarta. Jikinta mai tsarki ya saura har sai da idanuwa suka dauke sannan Imam Ali ya dora ta a kan wata makara da Asma'u bint Umais ta yi shi.
sannan shi, Hasan, Husaini, Ammar, Mikdad, Akil, Zubair, Abu Zarri, Salman, Baridah da wasu mutane daga Banu Hashim suka raka jikinta mai tsarki zuwa Makabartar Baki'a suka binne ta a can, suka kuma boye duk wata alamar kabarin don kar mutane su gane. An ruwaito cewa lokacin da Imam Ali (a.s.) ya saka Fatima a cikin kabari wani bakin ciki ya kara lullube shi, rabuwa da ita ya tsananta gare shi, matsayin ya yi matukar girmama a gabansa, sai ya fuskanci kabarin Manzon Allah (saw) don ya isar da kukansa, yana mai nuna irin kaunar da yake mata da cika wa babanta alkawari da bakin cikin rabuwa da ita da zafin abin da ya same shi tare da ita.
An ruwaito cewa a wannan lokacin Imam Ali (a.s) ya fuskanci inda Manzo (s.a.w.a) ya ke yayi sallama a gare shi da kuma bayyana masa
irin halin da suka shiga ciki bayansa da irin bakin cikin da ya same su sakamakon abubuwan da al'ummarsa suka aikata musu .
Haka Fatima al-Zahra ta rufe rayuwarta, don ta fara rayuwar dauwama a Firdausi, kuma don tarayu rayuwa har abada a lamirin tarihi da duniyar Musulunci a matsayin abin koyi da zukata ke daukaka da ita.
Amincin Allah ya tabbata a gare ki, Ya al-Zahra,karima yar MUHAMMADU rasulullahi saw.
ranar da aka haife ki, ranar da kika yi shahada
da kuma ranar da za a tashe ki kina rayayyiya
mai kai karan wadanda suka cuce ki wajen Allah
da ManzonSa.
Tabbas an zalunci ahalil baiti rasulullahi saw, Kuma muna tafe da ikon Allah.