@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TA HANYAR HARSHE AKE GANE HIKIMAR MAGANA
Yana daga cikin matsalar dake damun mutane wajen rashin karbar gaskiya ya zamana ta fito daga bakin wadanda ba sa so ta fito daga gare su.
Wannan kuwa na zai taba zama hujja gare su ba, domin babu wani da aka kebe shi cewa gaskiya daga gare shi kadai za a karbe ta. Lalle idan a kaga ko aka ji gaskiya ta fito daga mutum a karbeta kawai, kada a damu da cewa daga wajen wa ta fito.
Imam Ali (A. S) na cewa :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" خُذِ الْحِكْمَةَ مِمَّنْ أَتَاكَ بِهَا وَانْظُرْ إِلَى مَا قَالَ وَلَا تَنْظُرْهُ إِلَى مَنْ قَالَ."
" KA KARBI HIKIMA (gaskiya) DAGA WANDA YAZO MAKA DA ITA, KAYI DUBI ZUWA GA MENENE YACE BA, KADA KAYI DUBI ZUWA GA WANDA YA FADA (maganar). "
" Take wisdom from the one who brings it to you, and look at what he said, and do not look at who said it. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
A wani gurin kuma yana cewa:
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" الْحِكْمَةُ شَجَرَةٌ تَنْبُتُ فِي الْقَلْبِ وَتُثْمِرُ عَلَى اللِّسَانِ."
" ITA HIKIMA BISHIYA CE WACCE KE TSIROWA CIKIN ZUCIYA, KUMA TAYI 'YA'YA AKAN HARSHE. "
" Wisdom is a tree that grow in the heart and bears (it's) fruits on the tongue. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Saboda haka yayin da mu kaga gaskiya ta fito daga bakin Sayyid Zakzaky (H) sai kuma karbeta hannu bi-biyu (with open arms).
Ya Allah ka tabbatar damu kan wannan gaskiya.
🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
15th November, 2022/ 21st Rabi'us-Sani, 1444.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com