“Daya daga cikin abinda na sha nanata wa matasa shi ne kar
wani ya rudu da cewa wai sai ya tsufa zai yi addini. Don
mutane suna tunanin cewa nan gaba zasu yi addini, su yi ta
karatun Alkur’ani da sallar dare da addu’o’i idan sun tsufa. To
idan kaji wannan na shiga ranka, to shaidan ke maka wahayi.
Lokacin da ake da karfi ne ake ibada, in ka tsufa ba zaka iya
ba. Tsoho baya iya ibada, lokacin da kake jin karfi, lokacin
‘mujahada’ kenan lokacin sallar dare ke nan, lokacin karatun
Alkur’ani kenan, lokacin zaka iya. Idan ka tsufa baza ka iya ba.
Shine kuma zai sa a rubuta maka ladar abinda kake yi da karfi
don rashin karfi ya hana ka yi”.
“Amma idan ma baka yi, sai ka tsufa ka kasa, shi kenan ma
baka da wata lada. Amma idan dama kana yi, lokacin da kake
da karfi, alal misali lokacin da kake da karfi ka Saba duk karfe
biyun duniya kana tashi kayi sallah har gari ya waye, kuma kayi
ta’akibi har Rana ta fito; to sai tsufa ya Kama ka sai yazama
baza ka iya ba shi kenan sai ladarka ta cigaba kamar ka tashi
kullum-kullum, ko da ma baka tashi ba. Zai zama in dai tsufa
ya Kama ka ko gajiyawa, wato idan mutum ya tsufa yana jin
rauni ne a jikansa zai zama baya barci sosai, amma kuma
baida karfi na jiki.”
“Yanzu wasu abubuwa da muke yi da wasu abinciccika da
muke ci da ruwan da muke sha dama har da iskan da muke
sha duk an guggurbata. Nan da nan zaka ga mutane su hawan
jini din nan, Wanda ke jawo cututtukan jini iri-iri da rashin
motsa jiki, wanda yake sa nan da nan zakaga mutum ya shiga
kasala. Abubuwan da zai yi cikin kazar-kazar da karfin jiki
bayan ya shekara hamsin, sai kaga ya Fara kasawa. To saboda
haka lokaci ne na mujahada”.
—Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wani yanki na jawabin da ya
gabatar lokacin rufe mu’utamar Dandalin Matasan Harkar
Musulunci a Nigeria a muhallin ‘Fudiyya Islamic Center’ Zaria
shekarar 1436AH.
Daga Group din Tafseer da jawaban jagora
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com