DARASI: Sanin Allah Da Siffofinsa A Mahangar Ai'mmatu Ahlil Bait (AS)

FATIMATUZ ZAHRA (A.S)


Mai Gabatarwa :

Malam Ishaq Muhammad Kano


Wuri: KHAIRUL AMAL

(Whatsapp Group)


Yan uwa ina mika sallama da cewa: ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUH


To an ce in zabi Maudu'in da za a yi magana kansa a wannan lokaci ne, sai na zabi maudu'in: SANIN ALLAH DA SIFFOFINSA A MAHANYAR AHLUL BAITI (AS).


Na zabi farawa da wannan Maudu'i ne bisa la'akari da Muhimmancin sa da kuma gabatuwar sa akan duk wata makala ko ilimi da ya shafi addininmu na Musulunci.


Da farko zan fara da mabudi mai taken: MEYE MA'ANAR SANIN ALLAH? kuma MEYE MA'ANAR SANIN SIFFOFIN ALLAH SWT?


Yin bincike domin tabbatar da samuwar mahaliccin halittu, ta hanyar hujjoji na Hankali ba tare da dogara da wani ko wasu ba (Taklidi) a wajen gamsuwa da hakan.


Sanin Sifofin Allah Swt kuwa yana nufin: Tabbatarwa Allah Swt Siffofin da suka dace da Shi, da kuma kore masa Siffofin da suka koru gare Shi, kamar yanda ya Siffata Kansa da Kansa a cikin Littafinsa mai girma, ta hanyar tafsirin Manzo da Aimmatu Ahlil baiti suka yi wa ayoyin.


Wannan Maudu'i shine tushe ko asasi, ko asali na kowanne ilimi a cikin ilmomin addini. Kuma sai da shi ne ibadodi dukansu suke tsayawa, kuma suke samun karbuwa a wajen Allah swt.


Shi ya sa ma Imamu Ali (as) a Khudubar farko ta Littafin Nahjul balaga yake cewa:


"أول الدين معرفته"

.

"Farkon addini shine sanin Allah swt".


Wanda bai san Allah swt ba, ko kuma bai san shi ingantaccen sani ba, to ba zai san Manzonsa ba. Wanda bai san Manzo ba kuwa ba zai san Imamin zamaninsa ba. Wanda bai san Imamin zamaninsa ba kuwa zai kasa gane Lahira hakikanin ganewa, wato dai zai bace daga Hanya madaidaiciya, kamar yanda ya zo a addu'a Ma'athuriya cewa:


ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﺮﻓﻨﻲﻧﻔﺴﻚ ، ﻓﺈﻧﻚ ﺇﻥ ﻟﻢ ﺗﻌﺮﻓﻨﻲ ﻧﻔﺴﻚ ﻟﻢﺃﻋﺮﻑ ﺭﺳﻮﻟﻚ . ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﺮﻓﻨﻲ ﺭﺳﻮﻟﻚ ، ﻓﺈﻧﻚ ﺇﻥ ﻟﻢ ﺗﻌﺮﻓﻨﻲ ﺭﺳﻮﻟﻚ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺳﻠﻢ ، ﻟﻢ ﺃﻋﺮﻑ ﺣﺠﺘﻚ . ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻋﺮﻓﻨﻲ ﺣﺠﺘﻚ ، ﻓﺈﻧﻚ ﺇﻥ ﻟﻢ ﺗﻌﺮﻓﻨﻲ ﺣﺠﺘﻚ ﺿﻠﻠﺖُ ﻋﻦ ﺩﻳﻨﻲ .

.

"Ya Allah ka sanar da ni Kanka, saboda idan ba ka sanar da ni Kanka ba, ba zan san Manzonka ba.


Ya Allah ka sanar da ni Manzonka, saboda idan ba ka sanar da ni Manzonka ba, ba zan san Hujjarka ba.


Ya Allah ka sanar da ni Hujjarka, saboda idan ba ka sanar da ni Hujjarja ba zan bace daga addinina".


Ta hakan za mu ga cewa duk wanda ya kutsa a cikin bata, to ya kauce Sanin Allah swt ne.


*MUHIMMANCIN ILIMIN SANIN ALLAH SWT DA SIFFOFINSA:*


1. Yana kai mutum zuwa ga samun kololuwar Yakini.


2. Yana taimaka wa mutum wajen kawar da kowacce irin shubhar da masu kawo shubhohi ke kawo wa ta janibin Al'amarin Tauhidi.

Kamar cewa Tawassuli da salihan bayi Shirka ne.


3. Da sanin Allah ne mutum zai iya ajiye komai da kowa a muhallin sa, ba takaitawa ba kuma azarbabi. Ya san bawa ya san mahaliccin bawan, ya kuma san matsayin bawan daban, matsayin mahallicin bawan daban, bawa ba zai taba zama mahallici ba, kuma mahilicci ba zai taba zama halittacce ba, da sauran ire iren wadannan.


Yanzu kuma da Yardar Allah za mu dunguma cikin SANIN ALLAH SWT DA SIFFOFINSA.


Zan kawo Fakarar farko da Sheikh Muzaffar ya kawo a cikin Littafin Aka'idul Imamiyya, a babin da ya saka wa taken: AKIDARMU DANGANE DA ALLAH SWT


Zan kawo Fakarar farko da Sheikh Muzaffar ya kawo a cikin Littafin Aka'idul Imamiyya, a babin da ya saka wa taken: AKIDARMU DANGANE DA ALLAH SWT


Kuma a iya fakarar za mu tattauna a wannan satin, tare da kawo Sharhin wasu daga Siffofin Allah swt da aka ambata a Fakrar, a cikin hadisan Aimma (AS). Ga abin Sheikh Muzaffar yake cewa:


*KIDARMU DANGANE DA ALLAH SWT.*


Muna da Akidar cewa Allah ta'ala daya ne, (Wahidu) makadaici (Ahadu), komai bai yi kama da shi ba. Ba shi da farko, bai gushe ba kuma ba zai gushe ba.


Shine na Farko (Ba da faruwa ba), shine na karshe (Ba da karewa ba), Masani ne kuma Gwani, Adili ne kuma rayayye, mai iko ne, Mawadaci ne, mai Ji kuma mai Gani. Ba a siffata shi da irin abinda ake siffats bayi da shi


Saboda haka shi ba jiki ba ne, ba kuma Sura ba ne. Shi ba Jauhari ba ne, sannan shi ba Ard ba ne. Ba shi da nauyi ko rashin nauyi, ko motsi ko rashin motsi. Haka ma ba shi da Muhalli, ba shi kuma da Zamani, sannan ba a yin nune zuwa gare shi. Sannan ba shi da Tamka, ba shi da kamanni, sannan ba shi da Kishiya. Haka ma ba shi da Mata ba shi da d'a, kuma ba shi da abokin tarayya, Kuma babu ɗaya da ya kasance tamka a gare Shi. Gannai (Idanuwa) ba sa riskar Sa, amma shi yana riskar Gannai


Wannan ne karshen abinda za mu dan ce wani abu akai a yau


Yanzu za mu ji Sharhi daga Kalaman Aimma as, na wasu Siffofin Allah swt da muka gani a cikin wannan Babin


A cikin Karatun Shekh Muzaffar ya ambaci Sifar Allah ta WAHIDU


MEYE MA'ANAR 'WAHIDU' A HAKKIN ALLAH SWT?


Ma'anar واحد a Hakkin Allah swt shine: Wanda ba shi da kwatankwaci, kuma ba shi da tsara, kuma ba shi da abokin gwami.


Amma WAHIDU a Ma'anar Kidaya Wato 1,2,3,4,5,6..... Wannan ya koru ga Allah swt. Domin wanda ba na biyun sa ba zai shiga cikin Kirge (Lissafi) ba.


Haka ma WAHIDU a Ma'anar daya a cikin NAU'I, ko JINSI Shi ma ya koru ga Allah swt. Domin kuwa wanda ba bu irin sa, kuma babu kwatankwacin irin sa ba ya zama daya a cikin NAU'I ko JINSI.


MEYE MA'ANAR 'AHADU' A HAKKIN ALLAH SWT?


Ma'anar أحد Shine: Daya tilo wanda ba ya gutsuttsuruwa, kuma ba ya karbar rarrabawa a Zatinsa, ko a Sifofinsa . Ma'ana dai Zatin Allah swt makadaici ne, wato BASID ne ba MURAKKAB ba, wato ba bangarori ne suka taru suka zama shi ba, kamar yanda mutum yake.


Misali: Idan muka ce wane, kila mu ce sunansa "ALI", ka ga za mu fahimci cewa shi daya ne ba biyu ba, amma Zatinsa fa? Za mu ga yana da bangarori, kamar Jini, tsoka, Hannaye, idanuwa, Qashi, Qafafuwa, Kai, Kunnuwa da sauransu. Wadanda su bangarorin su ne suka hadu suka zama shi, kuma yana da bukata ga wadannan bangarorin nasa, wasu daga cikin bangarorin nasa idan ya rasa su zai tawaya ne ya samu Naqasu, wasu bangarorin ma yana rasa su, shi ma zai rasu, Kamar KAI misali. Saboda haka shi Mabukaci ne ga wadannan Bangarorin nasa da'iman.


To Shi Allah swt ba haka yake ba, Zatinsa AHAD ne, wato Zatinsa Makadaici ne, ba ya harhadu ba ne daga bangarori ko gabobi ko wasu abubuwan ba ne. Wato dai a turance za mu iya cewa Zatin Allah swt SIMPLE (بسيط) ne, ba COMPLEX (مركب) ba. Kuma Zatin nasa bai yi kama da wani abu ba, kamar yanda ya siffata kansa da hakan a cikin Littafinsa mai tsarki yana cewa:


ۚلَيْسَ كَمِثْلِهِ شَيْءٌ ۖ وَهُوَ السَّمِيعُ الْبَصِيرُ


"Wani abu bai yi kama da shi ba, kuma shi mai Ji ne kuma mai Gani" Suratus-Shura aya ta 11.


BANBANCI TSAKANIN AL-WAHIDU, DA AL-AHADU:


AL-WAHIDU SHINE: "Daya tilo wanda bai gushe ba shi shi kadai, kuma ba wani kwatankwacin sa tare da shi".


Littafin Furuqul-lugati na Sheikhul Jaza'iri Shafi na 37.


AL-AHADU SHINE: "Daya tilo wanda ba ya gutsuttsuruwa, kuma ba ya karbar rarrabawa a Zatinsa, ko a Siffofinsa".


Littafin Majma'ul bayan na Dabrasi juzu'i na 5 shafi na 564.


RUWAYOYIN DA SUKA ZO KAN MA'ANAR "AL-WAHIDU" DA "AL-AHADU" A HAKKIN ALLAH SWT:


Imamu Ali (as) ya fito mana da Ma'anar "WAHID" da "AHAD" a hakkin Allah swt, a cikin zancensa yana cewa:


"Shi (Allah swt) WAHIDU ne, ba shi da tamka a cikin abubuwa...... Kuma shi AHADIYYUL MA'ANA ne, bai rarrabu ba a cikin samuwar sa". (Wato shi ba Murakkab (Complex) ba ne.


Haka ma wani Balaraben Kyauye ya Tambayi Imamu Ali (as) a hanyar dawowar sa daga Yaqin Siffin, kan Ma'anar kasantuwar Allah swt "WAHIDU" (Daya) meye Ma'anar Wannan?


Sai Imamu Ali (as) yace da shi: Ya kai mai tambaya, hakika cewa Allah swt Daya ne ya kasu kashi 4 ne. Biyu daga ciki ba ya halasta a jingina su a hakkin Allah swt, biyu kuwa ana tabbatar da su a gare shi.


Biyun da ake kore su a hakkin Allah swt su ne:


1.Cewa Allah Daya ne da nufin babin Kidaya (1,2,3,4,5,...), Wannan ba ya halatta, saboda wanda ba shi da na biyu ba ya shiga cikin babin Kidaya. Ba ka ga cewa wadanda suka ce Allah swt na uku ne a cikin uku (Kiristoci) sun kafirta ba!.


2. Da fadar mai fadar cewa: Wane daya ne a cikin Mutane, wato yana nufin shi Nau'i ne a cikin Jinsi. Shi ma Wannan ba ya halatta a jingina shi a hakkin Allah swt, saboda Wannan Kamantawa ne, kuma Allah swt ya daukaka ga barin Kamantawa.


Amma biyun da ake tabbatar da su a hakkin Allah swt su ne:


1. Cewar mai cewa: Shi daya ne ba shi da kwatankwaci a cikin abubuwa, (Ma'anar Wahid) haka kuwa Ubangijinmu yake.


2. Cewar mai cewa: Shi Allah swt AHADIYYUL MA'ANA ne, wato yana nufin cewa ba ya rarrabuwa a cikin Kasantuwar sa.... (Ma'anar Ahad) haka kuwa Ubangijinmu yake mai girma da daukaka".


Littafin Tauhid na Sheikh Saduq Shafi na 84 babi na 3 Hadisi na 3.


Saboda haka a wannan Hadisin za mu koyi cewa Allah swt ba ya shiga a Lissafi, Kuma ba a hada shi tare da wani ko wasu a yi musu Ja'm'i. Misali: Ba a cewa Allah da manzonsa sun ce kaza, domin Allah swt ba ya shiga a cikin Lissafin Kirge, sai dai ka ce: Allah swt da Manzonsa ya ce Kaza, ko kuma ka ce: Allah ya ce kaza, haka ma manzo ya ce kaza, Amma ba a gwama Allah da wani a yi musu Jam'i.


A cikin Alkur'ani Allah swt ya koyar da mu Wannan Ladabin yana cewa a cikin Suratut-Tauba:


والله ورسوله أحق أن يرضوه إن كانوا مؤمنين.


"Allah da Manzonsa ne ya fi cancanta su nemi yardarsa in su sun kasance Muminai"


Za mu ga a nan Allah bai yi Tasniyar sunansa tare da na manzonsa ba, sai ya ce:

أن يرضوه


Bai ce: أن يرضوهما ba.


Saboda Allah ba ya shiga a cikin Lissafin Kirge. Kuma su Sayyid (h) sun yi ta koya mana Wannan Ladabin na rashin saka Allah swt a Lissafin Kirge, da sanya shi tare da wani ayi musu Jam'i, a cikin Karatuttukan Tafsiri da Nahjul Balaga.


MA'ANAR "AS-SAMI'U" (MAI JI), DA "AL-BASIRU" (MAI GANI):


Ya zo a cikin Littafin Tauhid na Sheikh Saduq, daga daya daga cikin A'imma (as) yana bayyana Ma'anar JI da GANI a hakkin Allah swt, yana cewa:


"Allah swt yana riskar komai amma fa ba da gabobi ba. Wato dai Allah swt ya san duk abinda ake idrakin sa ta hanyoyin da ake idrakin abubuwa guda biyar, (JI, GANI, DANDANO, SHAQA, DA TABA


Domin kuwa Allah swt ya tsarkaka daga ya kasance Jiki da duk abubuwan da ke lizimtar Jiki. Saboda haka Ma'anar fadar Allah swt da yake cewa dangane da Zatinsa mai tsarki: "Lalai shi mai ji ne kuma mai gani" Shine: Allah swt ya san duk abubuwan da ake ji, amma ba da kunne ba, kuma ya san duk abubuwan da ake gani, amma ba da Ido ba"


Wato dai za mu fahimci cewa Sifar Ji da Gani a hakkin Allah swt suna komawa ne ga Iliminsa ga dukannin abubuwa.

MEYE MA'ANAR "JAUHAR" DA "ARD", DA AKA KORE SU GA ALLAH SWT?


Ya gabata cewa Allah swt ba "JAUHAR" ba ne ba.


MA'ANAR "JAUHAR" LUGATAN SHINE: Hakikanin abu da kuma Zatinsa.


MA'ANAR "JAUHAR" A ISDILAHIN MALAMAN KALAM SHINE: Samammen da yake tsaye da Kansa, wato yana tsayuwa da Kansa ba tare da ya bukaci wani abu da zai tsaya da shi ko akan sa ba. Kamar Mutum da Dabbobi da ir-iren su. To Allah swt Shi ba "Jauhar" ne ba.


Ya gabata cewa kuma shi Allah swt ba "ARD" ba ne ba.


"ARD" Shine akasin "JAUHAR"


MA'ANAR "ARD" LUGATAN SHINE: Abinda ke bijirowa sai kuma ya gushe daga baya, kamar Rashin Lafiya, ko Rayuwar duniya, da sauran su.


Allah swt yayi amfani da wannan Ma'ana ta Luga a wurare da yawa a cikin Alkur'ani. Ga wasu ayoyin daga ciki:


فَخَلَفَ مِن بَعْدِهِمْ خَلْفٌ وَرِثُوا الْكِتَابَ يَأْخُذُونَ عَرَضَ هَٰذَا الْأَدْنَىٰ.


"Kuma sai masu mayewa suka maye a bayan su, sun gaji Littafin, Amma kuma suna karbar Tarkacen Wannan maqasqanciyar (Duniya). Suratul A'arafi aya ta 169.


A Wannan ayar sai Allah swt ya ambaci Duniya da jin dadin ta da Kalmar "ARD", saboda tana bijirowa sai kuma ta gushe bayan wani lokaci.


يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا ضَرَبْتُمْ فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَتَبَيَّنُوا وَلَا تَقُولُوا لِمَنْ أَلْقَىٰ إِلَيْكُمُ السَّلَامَ لَسْتَ مُؤْمِنًا تَبْتَغُونَ عَرَضَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا.


" Ya ku wadanda ku ka yi imani idan kuka yi Sara (Yaki) a Tafarkin Allah, Ku nemi bayani, kuma kada ku cewa wanda ya yi muku Sallama (Ya mika wuya ta hanyar furta Kalmar Shahada) kai ba mumini ba ne, kuna neman samun Tarkacen rayuwar Duniya"


MA'ANAR "ARD" A ISTIDAHI KUWA SHINE: Samammen da samuwar sa ta ke a ciki ko akan wani wabu. Wato shi ba ya tsayuwa da kansa sai da jinginuwa da wani abin. Kamar Launi, da Dandano, da Qanshi, da Zafi, da Sanyi. Za mu ga duka waddannan abubuwan, ba su tsayawa da Kansu, sai sun jingina kan wani Abu, ba kamar JAUHAR ba da shi ba ya bukatar jingina da wani abu a cikin tsayuwarsa da samuwar sa.


Misali: Idan muka kalli Allo Fari, to za mu ga abubuwa biyu ne, akwai Allo sannan akwai Fari, to shi farin shine "ARD" a nan, domin ba zai taba tsayawa da kansa ba sai da Allo din, wato yana bukatar Allon a wajen kasantuwar sa. Ba kamar "Jauhar" ba da shi tsayayye ne da kansa. To Allah swt Shi ba "Ard" ba ne ba. Kuma shi ba Jauhar ba ne.


MA'ANAR "ARD" A ISTIDAHI KUWA SHINE: Samammen da samuwar sa ta ke a ciki ko akan wani wabu. Wato shi ba ya tsayuwa da kansa sai da jinginuwa da wani abin. Kamar Launi, da Dandano, da Qanshi, da Zafi, da Sanyi. Za mu ga duka waddannan abubuwan, ba su tsayawa da Kansu, sai sun jingina kan wani Abu, ba kamar JAUHAR ba da shi ba ya bukatar jingina da wani abu a cikin tsayuwarsa da samuwar sa.


Misali: Idan muka kalli Allo Fari, to za mu ga abubuwa biyu ne, akwai Allo sannan akwai Fari, to shi farin shine "ARD" a nan, domin ba zai taba tsayawa da kansa ba sai da Allo din, wato yana bukatar Allon a wajen kasantuwar sa. Ba kamar "Jauhar" ba da shi tsayayye ne da kansa. To Allah swt Shi ba "Ard" ba ne ba. Kuma shi ba Jauhar ba ne.


MA'ANAR KORUWAR "ضد" WATO KISHIYA A HAKKIN ALLAH SWT


Kalmar "ضد" wato Kishiya, na da ma'anoni uku ne, kuma duk sun koru ga Allah swt, a bisa dalilai na hankali.


Ga ma'anonin guda uku:


1. Abubuwan da ba su haduwa a muhalli daya kuma a lokaci daya. Kamar Zafi da Sanyi, da Baqi da Fari. Wadannan kishiyoyin juna ne, ba su haduwa a wuri daya a cikin zamani daya. Irin Wannan Kishiyantaka ta koru a Hakkin Allah swt, saboda Allah swt ya daukaka daga ya zama Zamani ko Muhalli sun yi Tasiri a cikin sa, kamar yanda bayani ya gabata.


2. Abuwa biyu wadanda kowannen su yana da wani tasirin da ke daqile tasirin dayan. Kamar ruwa da Wuta. Za mu ga kowannen su idan ya hadu da dan uwansa yana hana shi yin tasiri. Saboda haka za mu ga cewa Ruwa da Wuta Koshiyoyin juna ne. Ita ma irin Wannan kishiyantaka ta koru ga Allah swt. Domin duk abinda ba Allah ba Halittace ne, kuma ba shi da cin gashin Kansa a cikin Samuwar sa, kuma zai zama samuwar sa ta tsayu ne da wanin sa, Saboda haka Mustahili ne ga duk wani abin halitta ya zama yana da wani Tasiri a kan Allah swt.


3. Abubuwa biyu wadanda daya daga cikin su, yana da Qarfi da kuma ikon hana dan uwansa. Kamar Mutane biyu su yi jayayya akan yin wani aiki iri kwaya daya, sai ya zama dayan ya fi dayan Qarfi, sai ya ture dan uwansa da Qarfi domin shi ya aikata Wannan aikin shi shi kadai. Ita ma irin Wannan kishiyantaka ta koru ga Allah swt, domin kuwa ba zai yiwu wani daga cikin halittun sa ya zama ya fi shi Qarfi ko ikon zartar da wani al'amari ko aiki ba.


A dubu Littafin Kashful muradi na Allama Hilli, Maqsad na 3, Fasali na 2 Mas'ala ta 11.


Da Idahul muradi na Ali Rabbani Al-Kalbakani Mas'ala ta 11 Shafi na 87.


Da Lawami'ul ilahiyya na Miqdad as-Suyuri Shafi na 406.


Ba a sifanta Allah swt da irin Siffofin da ake Sifanta Halittu da su.


Ruwayoyin da suka zo kan wannan:


ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : "ﻛﻞّ ﻣﺎ ﻓﻲ ﺍﻟﺨﻠﻖ ﻻ ﻳﻮﺟﺪ ﻓﻲ ﺧﺎﻟﻘﻪ" ‏( 4 ‏)


Imamu Ali (as) yana cewa: "Duk abinda yake a cikin halittu, (Na sura da jiki, da gabobi...), ba zai yiwu ya kasance ga Mahalicci ba".


Kitabut-Tauhid na Sheikh Saduq shafi ma 41, hadisi na


ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺟﻌﻔﺮ ﺑﻦ ﻣﺤﻤّﺪ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : "ﻛﻞّ ﺷﻲﺀ ﻭﻗﻊ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﺳﻢ ﺷﻲﺀ ﺳﻮﺍﻩ ‏[ ﺗﻌﺎﻟﻰ ‏] ﻓﻬﻮ ﻣﺨﻠﻮﻕ" ‏( 5 ‏) .


Imamu Sadiq (as) ya ce: "Duk wani abu da za a kira shi da sunan "ABU" idan ba Allah ba ne, to Wannan abin halittacce ne".


Kitabut-Tauhid na Sheikh Saduq shafi na 58 hadisi na 16


ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻣﺤﻤّﺪ ﺑﻦ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﺒﺎﻗﺮ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : "ﻣﺎ ﻭﻗﻊ ﻫﻤّﻚ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﻦ ﺷﻲﺀ ﻓﻬﻮ ﺧﻼﻓﻪ، ﻻ ﻳﺸﺒﻬﻪ ﺷﻲﺀ..." ‏( 6 ‏) .


An samo daga Imamu Bakir (as) ya ce: "Duk abinda tinaninka ya sawwala maka dangane da shi (Allah swt), to shi sabanin hakan ne, komai bai yi kama da shi ba"


Littafin Usulul Kafi na Sheikh Kulaini, shafi na 82 hadisi na 1.


ـ ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ﺑﻦ ﻣﻮﺳﻰ ﺍﻟﺮﺿﺎ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : " ﺇﺫﺍ ﺳﺄﻟﻮﻙ ﻋﻦ ﺍﻟﻜﻴﻔﻴﺔ، ﻓﻘﻞ ﻛﻤﺎ ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰّ ﻭﺟﻞّ : } ﻟﻴﺲ ﻛﻤﺜﻠﻪ ﺷﻲﺀ { ‏[ ﺍﻟﺸﻮﺭﻯ :11


An samo daga Imamu Rida (as) ya ce:


"Idan mutane suka tambaye ka yaya Allah swt yake? Ka ce da su: Kamar yanda Allah ya fada "ليس كمثله شيء" . "Komai bai yi kama da shi ba". Suratus-Shura aya ta 11.


Littafin Tauhid na Sheikh Saduq babi na 4, hadisi na 14Shafi na 92.


KORUWAR ZAMANI GA ALLAH SWT


Haka ma ba a siffata Allah swt da kasantuwa wani Zamani, domin kuwa shi kansa Zamanin Halittar Allah ne, kuma an Samar da shi ne.


Ya zo a ruwaya cewa: Wani Mutum ya tambayi Imamu Baqir (as) cewa: Ba ni labai dangane da Allah swt, yaushe ya kasance ne?


Sai Imamu (as) yace da shi: "Kaiconka!, kai kuma ba ni labari, yaushe ne bai kasance ba, da har zan ba ka labarin yaushe ya kasance?, Tsarki ya tabbata gare shi, bai gushe ba ba sai gushe ba har abada". Littafin Tauhid na Sheikh Saduq babi na 28 hadisi na 1, shafi na 168.


.ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : " ﺍlﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺍﻟﺬﻱ ... ﻟﻢ ﻳﺴﺒﻘﻪ ﻭﻗﺖ، ﻭﻟﻢ ﻳﺘﻘﺪّﻣﻪ ﺯﻣﺎﻥ " .


Imamu Ali (as) yana fada a wata Hudubarsa: "Godiya ta tabbata ga Allah, wanda lokaci bai rigaye shi ba, kuma Zamanin bai gabace shi ba".


Kitabut-Tauhid na Sheikh Saduq, babu na 2, Hadisi na 1, Shafi na 33.


2 ـ ﺳﺌﻞ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : ﻳﺎ ﺃﻣﻴﺮﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻣﺘّﻰ ﻛﺎﻥ ﺭﺑّﻨﺎ؟

ﻓﻘﺎﻝ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : .." ﺇﻧّﻤﺎ ﻳﻘﺎﻝ : ﻣﺘﻰ ﻛﺎﻥ ﻟﻤﻦ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻓﻜﺎﻥ، ﻫﻮ ﻛﺎﺋﻦ ﺑﻼ ﻛﻴﻨﻮﻧﺔ ﻛﺎﺋﻦ "... ‏( 3 ‏) .


An tambayi Imamu Ali (as) kan cewa: Yaushe ne Ubangijinmu ya kasance!?. Sai Imamu (as) yace: "Ana fadar yaushe ya kasance ne ga wanda bai kasance ba daga baya ya kasance. Shi kuma Allah swt, kasantacce ne ba tare da Kasantuwar da ta kasance ba".


Kitabut-Tauhid na Sheikh Saduq, babi na 27 Hadisi na 6, Shafi na


ـ ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺟﻌﻔﺮ ﺑﻦ ﻣﺤﻤّﺪ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : " ﺇﻥّ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﺒﺎﺭﻙ ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ ﻻ ﻳُﻮﺻﻒ ﺑﺰﻣﺎﻥ ... ﺑﻞ ﻫﻮ ﺧﺎﻟﻖ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ " ‏( 4 ‏) .

.

An samo daga Imamu Saduq (as) ya ce: "Hakika Allah swt ba a Siffata shi da Zamanin, domin kuwa shi ne Mahaliccin Zamanin".


Littafin AMALI na Sheikh Saduq, Majlisi na 47, Shafi na 353.


KORUWAR MUHALLI GA HAKKIN ALLAH SWT DA DALILI NA HANKALI:


Idan muka ce Allah swt yana a wani Muhalli ne, kamar mu ce SAMA masalan, to lazim Muhalli ya kasance ya siffatu da daya daga cikin abubuwa biyu:


1. Muhalli ya zama "Qadimi" ne, Wato ya zama ba shi da farko. Idan kuwa ya zama hakan to zai zama marashin farko ba daya ba ne, Wato muhallin ya zama wani ubangiji marashin farko kenan!, tunda rashin farko sifa ce ta Allah swt, Wannan kuwa ya sabawa hujjar hankali. Marashin farko dole ya zama daya ne ba biyu ba a bisa hujjar hankali, kuma shine Allah swt, shi shi kadai.


2. Muhallin ya zama "HADISI" ne, wato muhallin ya zama yana da farko, to shi kuma duk abu mai farko dole ya zama iyakantacce ne, wato yana da iyaka, shi kuma Allah swt ba shi da iyaka, abinda yake da iyaka kuwa ba zai yiwu ya kewaye abinda ba shi da iyaka ba. Saboda haka yi wa Allah Muhalli ya sabawa dalilai na hankali. Ana iya duba Littafin Kanzul Fawa'idi na Sheikh Abul fathi Al-Karajiki, juzu'i na 2 shafi na 104 domin ganin Karin bayanai


MUHALLI GA HAKKIN ALLAH SWT A RUWAYOYIN AIMMATU AHLIL BAITI (AS).


IMAMU ALI (AS) Yana fada a cikin wata hudubar shi a Littafin Nahjul balaga Huduba ta farko yana bayanin Allah swt yana cewa:


مَعَ كُلِّ شَيْ‏ءٍ لَا بِمُقَارَنَةٍ وَ غَيْرُ كُلِّ شَيْ‏ءٍ لَا بِمُزَايَلَةٍ.


"ALLAH swt yana tare da komai ba tareda Gwamuwa ba, kuma yana wajen komai ba tare da Rabuwa ba".


ﺳﺌﻞ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺟﻌﻔﺮ ﺑﻦ ﻣﺤﻤّﺪ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : ﻫﻞ ﻳﺠﻮﺯ ﺃﻥ ﻧﻘﻮﻝ: ﺇﻥّ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﺰّ ﻭﺟﻞّ ﻓﻲ ﻣﻜﺎ


ﻓﻘﺎﻝ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : "ﺳﺒﺤﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ ﻋﻦ ﺫﻟﻚ، ﺇﻧّﻪ ﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﻣﻜﺎﻥ ﻟﻜﺎﻥ ﻣﺤﺪَﺛﺎً; ﻷﻥّ ﺍﻟﻜﺎﺋﻦ ﻓﻲ ﻣﻜﺎﻥ ﻣﺤﺘﺎﺝ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﻤﻜﺎﻥ، ﻭﺍﻻﺣﺘﻴﺎﺝ ﻣﻦ ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻤُﺤﺪَﺙ ﻻ ﻣﻦ ﺻﻔﺎﺕ ﺍﻟﻘﺪﻳﻢ"


An tambayi Imamu Sadiq (as) cewa: Shin ya halatta mu yi tambaya kan cewa a wanne muhalli Allah swt yak


Sai Imamu (as) yace


"Subhanallahi wa ta'ala an zalika!, ai da a ce yana a wani Muhalli ne da ya zama fararre kenan, saboda duk wanda yake a wani Muhalli mabukaci ne ga Wannan Muhallin, bukata kuwa siffa ce ta fararre ba siffa ce ta wanda ba shi da farko ba


Littafin Tauhid na Sheikh Saduq babi na 28 hadisi na [6/2


ـ ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : ..." ﺇﻥّ ﺍﻟﻠّﻪ ﺟﻞّ ﻭﻋﺰّ ﺃﻳّﻦ ﺍﻷﻳﻦ ﻓﻼ ﺃﻳﻦ ﻟﻪ، ﻭﺟﻞّ ﻋﻦ ﺃﻥ ﻳﺤﻮﻳﻪ ﻣﻜﺎﻥ "... ‏( 1 


"An samo daga Imamu Ali (as) ya ce: "Hakika Allah swt shi ne ya samar da INA (muhalli) shi kuma ba shi da INA, ya daukaka daga muhalli ya tattara sh


Biharul anwar na Allama Majlisi, juzu'i na 57, Shafi na 8


2 ـ ﻗﺎﻝ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﻋﻠﻲ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : " ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﻣﻜﺎﻥ " ‏( 2 ‏)


A wani Hadisin Imamu Ali (as) yana cewa: "Allah swt yana nan tun babu Muhalli


Littafin Irshad na Sheikh Mufid, Juzu'i na 1, Shafi na 20


3 ـ ﻗﺎﻝ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺟﻌﻔﺮ ﺑﻦ ﻣﺤﻤّﺪ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : " ﻭﻻ ﻳﻮﺻﻒ ‏[ ﻋﺰّ ﻭﺟﻞّ ‏] ﺑﻜﻴﻒ ﻭﻻ ﺃﻳﻦ ... ، ﻛﻴﻒ ﺃﺻﻔﻪ ﺑﺄﻳﻦ ﻭﻫﻮ ﺍﻟﺬﻱ ﺃﻳّﻦ ﺍﻷﻳﻦ ﺣﺘّﻰ ﺻﺎﺭ ﺃﻳﻨﺎً، ﻓﻌﺮﻓﺖ ﺍﻷﻳﻦ ﺑﻤﺎ ﺃﻳّﻨﻪ ﻟﻨﺎ ﻣﻦ ﺍﻷﻳﻦ "... ‏( 3 ‏)


An samo daga Imamu Bakir (as) yana cewa: "Ba a siffata Allah da YAYA, ko INA, yaya kuwa zan siffata shi da INA alhali shine ya samar da INA har ta kasance INA, aka san INAR daga INAR da ya samar.


Littafin Kafi na Sheikh Kulaini Juzu'i na 1 shafi na 8


4 ـ ﺳُﺌﻞ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺟﻌﻔﺮ ﺑﻦ ﻣﺤﻤّﺪ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : ﺃﻳﻦ ﻛﺎﻥ ﺭﺑّﻨﺎ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﺨﻠﻖ ﺳﻤﺎﺀً ﺃﻭ ﺃﺭﺿﺎً؟ ﻓﻘﺎﻝ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) : " ﺃﻳﻦ ﺳﺆﺍﻝ ﻋﻦ ﻣﻜﺎﻥ، ﻭﻛﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﻻ ﻣﻜﺎﻥ " ( 4)


An tambayi Imamu Sadiq (as) kan cewa: A ina Ubangijinmu yake kafin ya halicci Sama da Kasa?. Sai Imamu (as) yace: "Me ya kawo tambayar Muhalli, alhali shi Allah yana nan tun babu Muhalli


Littafin Kafin na Sheikh Kulaini, juzu'i na 1, Shafi na 8


Na za mu tsaya lokaci na harara ta. Sharhin karatun bai kammalu ba sai dai wani Jikon idan Allah swt ya yarda. Za mu ga bayanin Koruwar Ganin Allah swt a nan duniya da kum a Lahira, a bisa dalilai na hankali da ruwayoyin Ai'mma AS.



DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM


@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/


@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/


DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN


@EMAIL: maasumalabari@gmail.com






Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post