Daga Halkar FIRJI Dake Da'irar Kazaure Ayau.

 


@_Ma'asuma Tv Nigeria News Update


Ayau Dadaran nan 'Yan uwa Almajiran Sayyeed Zakzaky (H) suka gabatar da Mauludin Fiyayyan Halitta Annabi Muhammad (Saww) na zaune acikin garin Firji kusa da Baban masallacin Juma'a na garin. Anfara wannan program din da karfe 9:00pm da 'yan mintuna.


 An gabatar da sha'iri Malam Aminu Kabara kazaure Inda ya zubo baitocin manzon Allah (saww) bayan ya Kammala sai aka gabatar da Malam Sa'adu kantama Wanda shine ya bude wurin da Addu'a bayan shima ya kammala sai aka gabatar da Dalibi Naseer Umar Alhassan Wanda shine ya gabatar da karatun Al Qur'ani mai girma. Daga nan kuma sai aka shiga Program gadan gadan Inda aka gabatar da Babban Bako mai Jawabi Ashsheik Hujjatul Islam Wal Musulumin Magaji Mai Wada Kazaure Wanda shine zai gabatar da jawabi agun.


Alhmdulillah Ashsheik Hujjatul Islam Wal Musulumin Magaji Mai Wada Kazaure ya fara da yiwa Allah (t) da kasance cewar sa a wanann wuri sai kuma ya yiwa 'yan uwa sallam ta Addinin Musulunci. Agaskiya Ashsheik Hujjatul Islam yayi jawabi sosai Inda ya faro tin daga salsalar Ma'aiki (Saww) da Kuma yadda ya isar da wannan sakon na addinin Musulunci zuwa ga Al'umma acikin jawabin sa ya fadawa 'yan uwa da kuma janyo hankali al'umma zuwa ga tafarkin gaskiya na Ma'aiki (saww) Inda ya kara da cewa idan mukayi da juriya da kisan da za'atayi mana da Kuma jarabawoyi to zamu Kai ga nasara Insha Allah saboda duk wani ilimin Technology dama sauran su wadan wadannan ya hudawan suke amfani dashi duk daga cikin Addinin mu suka same su kadan kenan daga cikin jawabin daya gabatar mana ayau 


Bayan ya kammala sai aka sake gabatar da Malam Sa'adu kantama Shima yada ce wani abu daga nan sai aka mayar da abinda magana zuwa ga Ashsheik Hujjatul Islam Wal Musulumin ya rufe taro da Addu'a acikin Addu'ar tasa yayiwa Jagoran mu Sayyeed Zakzaky (H) tare da mai dakin sa Ilahee ya kara musu lafiya da kariya 🤲 Sanna Kuma yayiwa 'yan uwa almajirin Sayyeed da sauran Al'ummar musulmi da Kuma halin da kasar take ciki sai aka sanar da cewa idan Allah ya tashe mu lafiya gobe da akwai Zagayen Muzaharar Mauludi Insha Allah anyi lafiya antashi lafiya


Naseer Umar Alhassan ✍️

25 November 2022

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post