DA'AWAR DA MUKE YI:

 


 ꜱʜᴀɪᴋ ɪʙʀᴀʜᴇᴇᴍ ᴢᴀᴋᴢᴀᴋy (ʜ)

Mu yanzu mene ne aikin mu a al'ummar nan da muka samu kan mu? Shiru za mu yi kowa ya yi ta kansa, ya je ya yi Sallarsa, albashi al'ummar ta gama lalacewa? Ko kuma za mu miƙe ne mu kira al'ummar mu ce a dawo ga addini? To wannan maganar da nake, gaskiyar magana ya fara tun a cikin ƙarshen Saba'noni ne, lokacin muna ɗalibai. To kuma ƙarshen Saba'nonin ne aka yi wata waƙi'ar da ta girgiza duniya, shi ne juyin Musulunci na Iran, a loƙacin da ake ganin kamar addini ya zama tsohon ya yi.

 “ Na'am akwai yunƙuri da aka rinƙa samu. An samu yunƙuri na mutane irin su Hassan Albanna ( Allah ya rahamshe shi ), wanda ya assasa ' Ikhwanul Musulunci', akwai kuma yunƙuri irin na su Sayyid Abul A'ala Maududi, wanda shi ma ya kafa ' jama'atul Islami', aka ja shi da ra'ayi ya shiga siyasa, aka tsaya takara. 'Jama'ati Islami',  ta zama jam'iyar Siyasa, La-samahallah, 'Blander' irin wannan ake gudun aikawa.

  “ To kuma shi ma irin wannan 'Blander',  'yan 'Ikhwan' sun auka masa, yayin da wani Sarki ( Faruƙ) ya ce zai yi shari'ar Musulunci, suka ce Masha Allah ! Suka yi masa mubaya'a, da irin waɗannan bilandodi. Sai ga juyi wanda ya fita daban, shi ne, juyin Imam Khomaini ( ƘS), shi bai faɗa tarko irin na siyasa ba, kuma ya tsaya ƙyam! To, sai ga shi kawai ya fitar da samfuri na irin da'awar Annabi (S) a wannan loƙaci, a yayin da mutane suke ganin kamar addini ba zai yiwu ya dawo ba.

To masha Allah, ka ga shikenan ma ga samfur mun gani, ba kawai abin da muke fatan zai yiwu, wasu suna ce mana ba zai yiyu ba, ga shi ya yiwu, akan idanun mu. Don haka ne ma kafircin duniya ya ankara da irin haɗarin juyin Musulunci na Iran zai kawo, ya ga cewa da can shi ya ɗauka ya gama da duniyar Musulmi. Ya ɗauka shikenan duniya ya riga ya mata ' Definition' Kuma an gama, shi musulunci ya koma babin abin da ya kira addini, 'Personal Affairs' tsakanin mutum da Ubangijinsa, ya riga ya ci duniya da yaƙi akan cewa yanzu duk nizamin da za a bi sunan shi rashin ruwa da addini, ya raba addini da siyasa, wato mulki daban siyasa daban.

 “ Addini ya taɓa mulki, amma a zamanin da ne, loƙacin da kai bai waye ba. Yanzu duniya ta cigaba, ba loƙacin yin wannan ne ba. Bilhasali ma mun taɓa yin taro irin wannan a jami'a, muka kawo cewa yadda addini ya kafu ya yi iko ( a baya ), har wani ya yi mana raddi,  da cewa eh an ji, addininku ya taɓa iko da duniya a wani loƙaci, amma loƙacin kai bai waye ba ne, a wannan zamani cigaba ne ba zai yiwu a dawo da addini ba, zamanin 'Science' da 'Technology' .

 “ To kama - kama da'awa tun zai yiwu ko ba zai yiwu ba. Har na karanta ' Article' ɗin wani, ya bani mamaki, shi ban ɗauka ma 'Symphatizer' bane, amma sai na ga ya rubuta 'article', amma na ga 'part one' ne, ya saka masa 'title' 'To be or not to be' wato zai yiwu ko ba zai yiwu ba. To sai ya ce a saurare shi a ɓangare na biyu. A ƙarshen ɓangaren na farkon, sai ya yi ishara ya zuwa ga wannan Harka.

faruq Sani Kudan 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post