NA SAN TAWILIN KOWACCE AYAR DATA SAUKA (in ji Imam Ali (A. S)) !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA ZA KUYI MIN BIYAYYA A BAYAN ANNABI (S. A. W. W) DA KUN AZURTU TA SAMA DA QASA
Rashin biyayya ga abinda Allah da Manzonsa (S. A. W. W) yayi umarci shine babban musabbabi/dalili na fadawar al'ummah cikin qunci da halin qaqa-ni-kayi. Da ace al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) sun riqi Imam Ali (A. S) a matsayin jagora bayan wafatin Annabi (S. A. W. W.) haqiqa da ta shiriya kuma ta azurta ta inda ba sa tsammani.
Tsaurin kan Yahudu da Nasara wajen qin aiki da littafin da aka saukar musu yayi sanadin wahalarsu, ko da kuwa kai a idonka kana gani suna cikin nutsuwa da wadata.
Allah (T) ne ya ambaci haka cikin littafinSa mai tsarki wanda za muga haqiqanin fassararsa/ma'anarta kamar haka :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
علي بن ابراهيم القمي (رحمه الله)- وَ لَوْ أَنَّهُمْ أَقامُوا التَّوْراةَ وَ الْإِنْجِيلَ وَ ما أُنْزِلَ إِلَيْهِمْ مِنْ رَبِّهِمْ يَعْنِي الْيَهُودَ وَ النَّصَارَي لَأَكَلُوا مِنْ فَوْقِهِمْ وَ مِنْ تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ قَالَ مِنْ فَوْقِهِمُ الْمَطَرُ وَ مِنْ تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ النَّبَاتُ قَوْلُهُ مِنْهُمْ أُمَّةٌ مُقْتَصِدَةٌ قَالَ قَوْمٌ مِنَ الْيَهُودِ دَخَلُوا فِي الْإِسْلَامِ فَسَمَّاهُمُ اللَّهُ مُقْتَصِدَةً.
Daga Aliyu Bn Ibrahim Al-Qummi (R. A) cikin fadin Allah (T) : " DA DAI ACE SUN TSAYAR DA ATTAURA DA LINJILA DA ABINDA AKA SAUMAR ZUWA GARE SU DAGA UBANGIJUNSU ."
Ana nufin Yahudu da Nasara, " DA KUWA SUN CI DAGA SAMANSU DA KUMA TA QARQASHIN QAFAFUNSU. "
Yace : " Ta saman nasu shine (a zubo musu ) ruwan sama (mai albarka), ta qarqashin qafafunsu kuma shine tsirrai. Fadinsa cewa :
" DAGA CIKINSU AKWAI AL'UMMA MATSAKAICIYA ." Yace : " Wata jama'a ce daga Yahudu wadanda suka shiga muslimci, sai Allah ya kira su da matsakaiciya /madaidaiciya ."
المصدر : بحارالأنوار، ج9، ص198/ العياشي، ج1، ص330/ البرهان - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج4، ص140
Kenan dole sai an bi hanyar daidai ake samun rabauta ko albarka dorarriya.
Imam Ali (A. S) na fada cikin gargadinsa ga 'Dalha yace :
أمير المؤمنين (عليه السلام)- أَنَّ أَمِيرَالْمُؤْمِنِينَ (عليه السلام) قَالَ يَا طَلْحَةُ إِنَّ كُلَّ آيَةٍ أَنْزَلَهَا اللَّهُ عَلَى مُحَمَّدٍ (صلى الله عليه و آله) عِنْدِي بِإِمْلَاءِ رَسُولِ اللَّهِ (صلى الله عليه و آله) وَ خَطِّي بِيَدِي وَ تَأْوِيلَ كُلِّ آيَةٍ أَنْزَلَهَا اللَّهُ عَلَى مُحَمَّدٍ (صلى الله عليه و آله) وَ كُلَّ حَلَالٍ وَ حَرَامٍ أَوْ حَدٍّ أَوْ حُكْمٍ تَحْتَاجُ إِلَيْهِ الْأُمَّةُ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ عِنْدِي مَكْتُوبٌ بِإِمْلَاءِ رَسُولِ اللَّهِ (صلى الله عليه و آله) وَ خَطِّي بِيَدِي حَتَّي أَرْشَ الْخَدْشِ قَالَ طَلْحَةُ كُلُّ شَيْءٍ مِنْ صَغِيرٍ أَوْ كَبِيرٍ أَوْ خَاصٍّ أَوْ عَامٍ أَوْ كَانَ أَوْ يَكُونُ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ فَهُوَ مَكْتُوبٌ عِنْدَكَ قَالَ نَعَمْ وَ سِوَي ذَلِكَ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ (صلى الله عليه و آله) أَسَرَّ إِلَيَّ فِي مَرَضِهِ مِفْتَاحَ أَلْفِ بَابٍ فِي الْعِلْمِ يَفْتَحُ كُلُّ بَابٍ أَلْفَ بَابٍ وَ لَوْ أَنَّ الْأُمَّةَ بَعْدَ قَبْضِ رَسُولِ اللَّهِ (صلى الله عليه و آله) اتَّبَعُونِي وَ أَطَاعُونِي لَأَكَلُوا مِنْ فَوْقِهِمْ وَ مِنْ تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ.
" Yaa 'Dalhatu ! Lalle kowacce aya wacce Allah ya daukar da ita ga Muhammadu (S. A. W. W) tana wajena da siffar Manzon Allah (S. A. W. W) da kuma rubutuna da hannuna.
Kuma tawilin kowacce aya (sanin ma'anoninta mabambanta) wacce aka saukar da ita ga Muhammadu (S. A. W. W) , da kuma kowanne haram da halal ko kuma haddi ko kuma hukunci wanda al'umma ke buqatuwa zuwa gare shi har ranar alqiyama (don sanin hukuncinsa) nanan rubuce a wajena da siffar Manzon Allah (S. A. W. W) kuma rubutun da nayi da hannuna har qarshen rayuwa. "
Sai 'Dalhatu yace : " Kowanne abu daga qarami ko babba ko kebabbe ko na gaba daya (Amm) ko wanda ya kasance ko wanda zai kasance (nan gaba) zuwa ranar alqiyama nanan rubuce tare da kai? " Yace :
" Eh (yana nan tare dani), da ma koma-bayan haka, lalle Manzon Allah (S. A W. W) ya asirta min cikin jinyarsa (wacce ya bar duniya) wasu qofofi dubu na babukan ilimi. Kowanne babi na bude babuka dubu (babi dubu sau dubu kenan wanda ke daidai da babuka miliyan na ilimi) . Da ace bayan karbar ran Manzon Allah (S. A. W. W) al'umma ta bi ni kuma tayi min biyayya, haqiqa da sunci daga samansu da ma ta qarqashin qafafunsu. "
المصدر : بحارالأنوار، ج26، ص65 - تفسير أهل البيت عليهم السلام ج4، ص140
Wannan shine Imam Ali (A. S) wanda al'umma tayi hasara sakamakon rashin yin biyayya gare shi da kuma rashin binsa.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda .
(08137925034)
30th November, 2022/ 6th Jimada-Ulah, 1444.