- Sheikh Ibrahim Zakzaky
Addu'armu ita ce duk wanda ya shirya mana sharri, mu ba tunanin mu yi masa sharri ba ne, muna rokon Allah ya mai da sharrin kansa. Muna rokon Allah ne duk wani lokacin da wani ya harbo bindiga, ya juya harsashin zuwa kirjinsa. Abin da mu ke fata kenan. Rokonmu kenan kuma Alhamdulillah Allah yana amsa rokonmu. Saboda haka zo ka harba! Ka harba kan ka dai! In kana so ka mutu, ka zo kayi fada da mu! In kana so ka yi mummunan karshe ka zo kayi fada da mu! In kana so mulkinka ya rushe, zo ka yi fada da mu! Eh mana! Mu in an yi fada damu ne muke yin karfi ai. Wannan taron saboda menene muje yi? Ba saboda an kashe mana 'yan uwanmu bane? To ai albarkacinsu muke ci. Saboda haka bismillah! Ga fage, ga mai doki! Baza mu fasa abin da muke ba, ku ma kar ku fasa!
— Sheikh Zakzaky (H) a taron Yaumu Shuhada a garin Zaria ranar 22/Rajab/1434.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com