KIN SAN WANENE MIJI NAGARI KUWA?!
-
Ba sai lallai mai tarin dukiya ne kaɗai yake zamtowa miji nagari ba.
-
Ba sai lallai wanda ya iya kalaman soyayya bane kaɗai yake zamtowa miji nagari ba.
-
Ba sai lallai wanda zai ke biya miki dukkanin buƙatunki bane yake zamtowa miji nagari ba.
-
🕳️Miji nagari shine wanda yake ɗoraki akan biyayyar Allah.
-
🕳️Miji nagari shine wanda koda yaushe zai ke tunatar dake lamarin Allah.
-
🕳️Miji nagari shine wanda yake tsoron Allah, kuma yake sauke miki duk wani haƙƙin da ya zama wajibi a rayuwar aurenku.
-
Kada ki ƙwallafa rai akan cewa ke lallai sai mai tarin kuɗi, domin shi arziƙi nufi ne na ubangiji Allah.
-
Idan kika zamto mai biyayyar aure, komai talaucin mijinki sai kiga kun taru kun haifar da gida nagari.
-
Amma idan kika kasance mai yawan kwaɗayin abin duniya, to lallai zaki dauwama cikin wahala da kuma rashin godiyar ubangiji maɗaukakin sarki.
-
Ƴar'uwa mai albarka!, ya zama wajibi akan ki tsaya ki nutsu kisan cewa ba komai bane a wannan duniyar face ruɗu da yaudara, haƙurinki a gidan miji zai iya haifar miki dauwamamman jin daɗin lahira.
-
Ya Allah kasa mudace, Ameen.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com