BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Da yawan wasu ƴan matan sun ɗauki aure a matsayin tamkar wani abun gasa ne wanda in wance bata yi ba, to shi kenan an sami abun yi mata gori"
-
"Wasu ƴan matan kuma za suyi aure, amma basu san darajar auren ba, za ka ga suna raina matsayin aurensu, sukan ji tamkar su ba matan aure bane sabida da basu yi ilmin auren ba"
-
"Wasu kuma sun san cewa haƙiƙa aure bauta ne a garesu, sabida haka su sun zo yin bauta ne gidan mijinsu, kuma sun san cewa haƙiƙa sun sami ƴanci fiye da wanda suke dashi a gidajen iyayensu"
-
"Aure ƴanci ne a gareki, kiyi ƙoƙari ki zauna a gidan mijinki koda kuna da yawa a gurinsa, ki zamto mai biyayyar aure, kada ki zamto mai wulaƙanta zamantakewar aure. Da yawan ƴan mata a waje suna son su taka irin matsayin da kika ta ka na yin aure, amma basu sami dama ba, to ke da kike da auren kiyi ƙoƙari ki riƙe kayanki ta hanyar yin gaskiya da adalci da kuma kyautata dukkanin haƙƙoƙin mijinki"
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com