AURE BA KASUWANCI BANE!!!


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE 



Mafi yawa abinda yake damun akasarin matan yanzu kenan, buri, kwadayi da son zuciya, da kuma son abin duniya wajan neman abokin rayuwa.

  Ta yaya za mu iya jure rufin asirin iyayen mu amma akan abokan rayuwar auren mu sai mu rufe ido mu zama masu buri, da kwadayi, wani burin ma sai ka rasa ta yadda aka lissafa shi.

A lokuta da dama a yanzu, wasu iyaye mata plays a vital role wajan nuna wa yarinyar su cewa itafa matar manya ce ( ma'ana matar mai kudi) Sam ba'a duba ganarta sa nalle mutunci, sai kaji ana cewa , gwanda kije gidan da zaki huta muma mu huta, a nasu ganin kenan, bacin aure ibada ne ba kasuwanci ba, ana Gina aure ne bisa turbar soyayya, kyautatawa, farin ciki, da kuma fatan samun albarka na zuri'a, amma yanzu idan mu ya rufe sai mai kudi , hmmm to akwai Mata da yawa da suke kukan aure a ire iren wadan nan gidajen, suna da damuwoyi da yawa , Wanda kudi baya iya samar musu, babban abinda zakaji suna complain akai shine rashin lokaci ko cikakken kulawa daga wajan miji, Wanda suma wadan nan abubuwa guda biyun suna daga cikin abinda yake saka aure yayi dadi ko akasin haka, to ta yiwu ga kudin babu kwanciyar hankali ko babu jin dadi , to ta yaya za'ayi rayuwar farin ciki? 

 Indai har akwai soyayya da kauna, kuma miji zaiyi iya bakin kokarin shi wajan miki abubuwan da suka zama wajibi a gare shi kamar ci, sha, sutura, tufafi, rashin lapiya da sauran su, sai kuma kyautatawa da abubuwan da zai iya , amma yanzu kam tunanin mu yafi karfin nan, kwakwalwar mu bata hango wadan nan sai abinda yake a chan sama, 

  Kuma a wajaje da yawa sai kaga namiji yana lallaba rayuwar shi da matarsa baka San irin wahalar da ya sha Kafin ya tara ba amma tashi daya sai kaga yarinya ita ala dole sai ta shiga tafi matar shi ta ciki moriyar shi, 

Ire iren burikan da muke yi a yanzu ko kuma ince muke dasshi, da karya, ga kuma rashin neman zabin Allah shine yake kara haddasa mana matsaloli amma mun kasa fahimta. 

Ina mafita a nan? 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post